Rahotanni daga sassan Najeriya sun nuna da dama daga cikin daliget na jam’iyyun siyasa sun jiku da Naira, a wasu wuraren ma da Dala aka jika su, albarkacin zabubbukan fidda gwanin da jam’iyyun suka gudanar.
Kafin zabubbukan, an ji, an kuma karanta a jaridu da sauran kafafen yada labarai yadda ’yan takara a jam’iyyu daban-daban suka yi ta cika wa daliget aljihu da kudi don neman kuri’a.
- ‘Duk yadda sakamakon zaben fidda gwanin APC ya kasance zan karbe shi hannu biyu’
- Ayyukan da Buhari ya aiwatar a Spain kafin dawowarsa Najeriya
Da alama dai wananan al’amari ya yi wa daliget din dadi matuka, inda wasunsu ke ci gaba da fantamawa da kuma more kudin da suka samu daga ’yan takara.
Ko a baya-bayan nan, an ga hotunan yadda wani daliget daga Jihar Kaduna, Rossi Tanko Sabo, ya raba wa jama’ar yankinsu kudaden da masu neman takara suka ba shi gabanin zaben fitar da dan takara.
Rossi Tanko Sabo Rossi, wanda daliget ne a zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP wanda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya lashe, ya raba Naira miliyan bakwai da ya samu ga talakawa a Karamar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.
Ta leko ta koma
Sai dai kuma, a daidai lokacin da daliget a wasu jihohi ke ci gaba da shakatawa da ‘hatimin nasaran’ da suka samu, a Jihar Neja kuwa, a Karamar Hukumar Bosso ta jihar, labarin ya bambanta.
Wani dan takara na jam’iyyar PDP ya bukaci daliget su maida masa kudadensa bayan da ya fadi zaben fitar da dan takara da jam’iyyar ta gudanar a jihar.
Barista Abbas Bello, tsohon kwamishina ne kuma tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Neja, yana daga cikin ’yan takarar Majalisar Wakilai ta Kasa a mazabar Bosso/Paikoro a karkashin Jam’iyyar PDP.
Dan takarar ya bukaci daliget na mazabar tasa su maida masa kudaden da ya raba musu tun da sun kasa cika alkawarin su zabe shi yayin zaben fidda gwanin da jam’iyyarsu ta PDP.
An gano hakan ne bayan da wani bidiyo da aka yada a kafafen sadarwa na zamani ya nuna yadda darakatan yakin neman zaben dan takarar ya zauna yana karbar kudaden da daliget din suka dawo da su a cikin ambulan.
Bidiyon ya nuna yadda daliget na gundumomin mazabar suka yi ta dawo da Naira dubu dari uku-ukun da Abbas Bello ya raba musu a kan su zabe shi.
Gundumomin sun hada da: Maikunkele, Bosso Central I, Bosso Central II, Chanchaga, Maitumbi, Kampala, Garatu, Kodo, Shata da kuma Beji.
Ya zuwa hada wannan rahoton, duka gundumomin sun maida wa dan takarar kudinsa in banda gundumar Shata da Beji da suka rage.
Majiya ta kusa da daliget din da lamarin ya shafa ta yi zargin cewa karancin kudaden da dan takarar ya bayar ne ya sa daliget din suka juya masa baya.
An ji wakilin dan takarar na cewa, “Gyara muke so a yi a kasa, kuma da haka za a fara gyaran.”
Saura daliget din APC
A hannu guda, ana rade-radin irin wannan mataki na bukatar maido da kudadensu da wasu ’yan takara kan yi sakamakon shan kaye a zaben fitar da gwani ka iya shafar wasu daliget na Jam’iyyar APC a Jihar ta Neja.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa akwai jita-jitar daya daga cikin ’yan takarar gwamnan jihar a APC shi ma ya ce wasu daga cikin wadanda suka yi masa aikin neman kuri’a su dawo masa da kudadensa.
A cewar majiyar, ya bukaci hakan ne bayan da ya fadi zaben fitar da dan takarar da zai tsaya wa APC takarar gwmana a jihar.
Majiyar ta ce miliyoyin Naira dan takarar ya ware ya mika wa wasu jiga-jigan APC a jihar don su yi masa aikin cin zaben, amm a karshe kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Shin za a dawo da kudaden?
Ta kara da cewa, idan ta tabbata dan takarar ya bukaci su maida masa kudinsa, to fa daliget da aka raba wa kudaden su dawo da abin da aka bai wa kowannensu.
Yayin da wasu daliget kan dau kaddara su mayar da kudin da aka ba su idan aka bukaci hakan daga gare su, wasunsu kuwa cewa suke ko da sama da kasa za su hade, babu dan takarar da ya isa ya tilasta musu maida masa kudadensa tun da ba su suka jawo shi ba.
Amfani da kudi wajen neman kuri’a dai ya zama wata babbabr al’ada a siyasar Najeriya, lamarin da masana da manazarta ke ganin babbar illa ce ga sha’anin siyasa.
A cewar masanan, muddin ba a kawar da wannan mummunar al’adar ba, da wahala a samu siyasa mai tsafta a kasar.