✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Edo: ’Yan sanda za su kwace haramtattun makamai

Ya zama dole ganin yadda ’yan bangar siyasa da wasu miyagu ke daukar makami a lokutan zabe

Rundunar  ’Yan Sandan Najeriya ta umarci kwamishinoninta na jihohi cewa nan take su binciko su kuma kwace dukkannin makamai da ke hannun mutane ba bisa ka’aida ba.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya kuma umarce su da su gurfanar da wadanda aka samu da haramtattun makaman a gaban kuliya.

Kakakin Rundunar, Frank Mba ya ce umarnin na zuwa ne gabanin zaben gwamnan jihohin Edo da Ondo da kuma yaki da yaduwar haramtattun makamai a Najeriya.

Sanarwar ta ce hakan ya zama wajibi la’akari da yadda ’yan bangar siyasa da sauran miyagu ka daukar makamai musamman a lokutan zabe.

Shugaban Rundunar ya umarci kwamishinonin su yi tarukan wayar da kai nan take ga sauran jami’an tsaro kan yadda za su yi aiki cikin doka.

Hakan na da nasaba da yadda jami’an kungiyoyin tsaro da ’yan banga ke daukar makamai bisa dalilai marasa tushe.

Ya ce hakan ya saba doka kuma idan ba a yi saurin magancewa ba zai sama barazana ga tsaron kasa.

Shugaban ’Yan Sandan ya kuma roki ’yan Najeriya da su ba wa jami’ansa hadin kai wajen gudanar da aikin domin kare rayuka da dukiya a fadin kasa.