✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Edo: Ize-Iyamu ya lashe zaben fid da gwanin APC

Osagie Ize-Iyamu ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo da ke tafe bayan ya lashe zaben fid da gwani…

Osagie Ize-Iyamu ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo da ke tafe bayan ya lashe zaben fid da gwani na jam’iyyar.

Ize-Iyamu shi ne na hannun daman Shugaban Jam’iyyar APC da aka dakatar Adams Oshiomhole, a zaben da ke tafe ranar 19 ga watan Satumba.

Shugaban Kwamitin Zaben Dan Takarar kuma Gwamnan Imo Sanata Hope Uzodimna ya sanar cewa Ize-Iyamu ne ya lashe zaben bayan ya kayar da abokin karawarsa, tsohon mataimakin gwamnan jihar Pius Odubu.

Uzodinma ya ce Ize-Iyamu ya lashe zaben ne a dukkan kananan hukumomi 18 na jihar, inda ya samu mafi yawan kuri’u.

“Iyamu, bayan ya sami kuri’u mafiya rinjaye, ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna mai zuwa”, inji shi.

Da yake wa ‘yan jarida jawabi bayan sanar da sakamakon zaben, dan takarar ya ce yana da kwarin gwiwar jam’iyyarsu ce za ta yi nasara a zaben mai zuwa.

Zaben fidda dan takarar jam’iyyar a zaben da ke tafe ya dade yana tayar da kura, har ta kai ga gwamnan jihar Godwin Obaseki ya fice daga jam’iyyar bayan ta hana shi neman takara.

Jam’iyyar ta hana sauran ‘yan takara 3 da suka nemi shiga zaben fidda gwanin inda ta bar Pius Odubu da Ize-Iyamu, a wani abu da ake ganin tamkar tadiye sauran ne domin ganin dan gaban Oshiomholen ya samu tsayawa takara.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa akwai jami’an Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da suka kasance suna sa’aido a wajen zaben da kuma jami’an tsaro da aka jibge a wurin don tabbatar da doka da oda.