✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Edo: An jibge karin jami’an tsaro 13,311

Hukumar tsaro ta NSCDC ta ce kimanin jami’anta 13,311 daga jihohi 13 ne ta jibge a Jihar Edo domin shirye-shiryen zaben gwamna ranar Asabar. Mataimakin…

Hukumar tsaro ta NSCDC ta ce kimanin jami’anta 13,311 daga jihohi 13 ne ta jibge a Jihar Edo domin shirye-shiryen zaben gwamna ranar Asabar.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar mai kula da Sashen Ayyuka, Madu Kelechi ya bayyana hakan a birnin Benin na jihar lokacin da yake yi wa ‘yan jarida jawabi kan shirye-shiryen zaben.

Ya ce daga cikin adadin, jami’ai 7,331 za su shiga harkar zaben ka’in da na’in, yayin da za a tura ragowar domin kare muhimman kadarorin gwamnati a sassan jihar.

Modu ya ce jami’an hukumar za su yi aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin zaben.

Ya tabbatar da cewa hukumar a shirye take kuma ta horar da jami’an nata dabaru daban-daban ciki har da na kiyaye dokokin COVID-19 kasancewar za a gudanar da zaben ne cikin tsauraran matakan kariya daga cutar.

Ya ce an kuma ja kunnen jami’an yadda ya kamata wajen kiyaye mutuncinsu da kuma tabbatar da cewa an bi ka’ida musamman wajen kaucewa sayen kuri’u.

A ranar Asabar ce za a kece raini a zaben da alamu suka nuna fafatawa za ta fi zafi tsakanin gwamna mai ci, Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP da kuma Osagie Ize-Iyamu na APC.