Wasu da ake zargi ’yan bindiga ne a ranar Asabar sun kawo hargitsi a yayin zaben cike gurbi na ’dan majalisar dokokin jihar Zamfara da ake gudanar wa a kauyen Oriji na gundumar Rini da ke karkashin Karamar Hukumar Bakura.
Wani da ya fito kada kuri’a mai suna Suleiman Muhammad Rini, ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 8.00 na safe yayin da ma’aikatan zaben suka isa rumfar zaben domin fara aiki, sai ga wasu gungun mutane dauke da makamai ba zato ba tsammani sun fito daga wani daji kuma suka nufi wurin zaben.
- Buhari ya yi alhinin mutuwar Janar Domkat Bali
- Matsalar Tsaro: Za mu gana da Buhari — NGF
- ‘Addu’o’i ne za su kawo karshen ta’addanci a Arewa’
“Da mu da jami’an zaben duk muka arce don neman mafaka amma daga bisani jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda sun yi gaggawar kawo dauki wurin bayan an ankarar da su halin da ake ciki.”
“Sun samu nasarar fatattakar ’yan bindigar kuma tuni zabe ya kan kama,” inji Suleiman.
A yayin haka kuma mun samu cewa sai da jami’an tsaro suka rika harbi cikin iska domin tabbatar da an kiyaye doka da oda a rumfar zabe mai lamba ta takwas a shiyyar Galadima da ke kauyen na Rini.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya wakana ne a yayin da wasu bata-gari suka yi yunkurin kawo hargitsi ana tsaka da gudanar da zabe.
Hargitsin ya faru ne bayan da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu, Alhaji Yahaya Chado Gora da Tsohon Kwamishinan Ma’aikatar, Alhaji Muttaka Rini da Mataimakiyar Shugabar Jam’iyyar PDP ta jihar, Hajiya A’I Maradun suka isa wurin zaben.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da tarzoma ta lafa kuma an ci gaba da gudanar da zaben cikin salama.