Kasar Amurka ta yi barazanar hana ba da izinin shiga cikinta (biza) ga duk wanda ya yi kokarin ta da zaune tsaye a zaben Gwamnan Jihar Anambra na ranar Asabar.
Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya ya fitar a Abuja ranar Laraba.
- Kotu ta daure magidancin da ya ‘zagi’ Ganduje a Facebook
- Yadda N200 ta yi sanadin mutuwar masu tura baro 2 a Aba
Sanarwar ta kara da cewa, “Amurka na fatan ganin an yi zaben Gwamna a Jihar Anambra ranar shida ga watan Nuwamba lami lafiya, cikin adalci sannan sakamakonsa ya yi daidai da muradun ’yan Jihar.
“Za mu sanya ido sosai kan mutanen da za su yi yunkurin katsa-landan ga harkokin Dimokradiyya, ko su ta da rikici kafin zabe, yayin zaben da kuma bayan kammala shi.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukar tsauraran matakai, ciki har da na hana bayar da biza, ga duk wanda muka gano yana da hannu a kokarin kawo rikici.
“A karkashin dokokin shige da fice na Amurka, akwai laifukan da za su kai ga hatta iyalan mutum su ma a hana su.
“Muna kira ga ’yan kasa, malaman zabe da jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an yi ingantaccen zabe,” inji sanarwar.