Dan takarar jam’iyyar APGA a zaben gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, na ci gaba da yin zarra a yawan kuri’u da Kananan Hukumomi.
Sakamakon da aka bayyana zuwa yanzu ya nuna Farfesa Soludo, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya lashe kananan hukumomi 12.
Sai dai dan takarar jami’yyar YPP, Sanata Ifeanyi Ubah, ya fita kunya, ya lashe karamar hukumarsa ta asali, Nnewi ta Aewa.
Kananan Hukumomin da aka sanar Soludo ya lashe sun hada da Orumba ta Arewa, da Orumba ta Kudu, da Njijoka, da Awka ta Kudu, da Onitsha ta Kudu, da Anambra ta Gabas, da Anaocha, da Aguata.
Sauran su ne Dunukofia, da Ayamelum, da Oyi, da Idemili ta Kudu, da kuma Nnewi ta Arewa.
APC, PDP ba labari
Kawo yanzu dai babu ko daya daga cikin jam’iyyu mafiya rinjaye a Najeriya na PDP da APC da ta lashe zaben ko da karamar hukuma daya a sakamakon da aka sanar.
Aminiya za ta ci gaba da kawo muku sakamakon zaben kai tsaye daga hedkwatar Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, da ke Awka, babban birnin Jihar Anambra.
A halin yanzu ga sakamakon zaben kananan hukumomin da aka sanar:
Orumba ta Arewa
APC: 2, 692
PDP: 1,863
APGA: 4,826
Aguata
APC: 4,773
PDP: 3,798
APGA: 9,136
Njikoka
APC: 3,216
PDP: 3,409
APGA: 8,803
Orumba ta Kudu
APC: 2,060
PDP: 1,672
APGA: 4,394
Awka ta Kudu
APC: 2,595
PDP: 5,489
APGA: 12,891
Onitsha ta Kudu
APC: 2,050
PDP: 2,253
APGA: 4,281
Anambra ta Gabas
APC: 2,034
PDP: 1,380
APGA: 9,746
Anaocha
APC: 2,085
PDP: 5,108
APGA: 6,911
Dunukofia
APCL 1,991
APGA: 4.124
PDP: 1,680
Ayamelum
APC 2,409
APGAL 3,424
PDP: 2,804
Oyi
APCL 2,830
APGAL 6,133
PDPL 2,484
Idemili ta Kudu
APC: 1,039
APGA: 2,312
PDP: 2,016
Nnewi ta Arewa
APC: 1,278
APGA: 3,369
PDP: 1,511
YPP: 6,485