Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta aike muhimman kayan zaɓe da za a yi amfani da su a zaɓen Gwamnan da za a gudanar a Jihar Ondo, a ranar Asabar mai zuwa.
INEC, ta sanar a shafinta na X (Twitter), a ranar Litinin cewa, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ce, ta taimaka wajen jigilar kayan, kuma jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN), za su karɓe su da zarar sun isa jihar.
- Gawuna ya fi dacewa a bai wa muƙamin minista — Gwarzo
- Za a yi jana’izar Babban Hafsan Sojin Ƙasa a ranar Juma’a
Sanarwar ta ce, “Labari Cikin Gaggawa! Kayan zaɓen gwamnan Jihar Ondo masu muhimmanci, wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba 2024, sun isa Akure.
“Sun isa babban birnin jihar, kuma jami’an Babban Bankin Najeriya ne za su karɓe su.
“Rundunar Sojin Sama na Najeriya ne, suka kai kayan zuwa Akure.”
Ga hotunan a ƙasa: