- Rashin umarnin kotu ya haifar da fargaba a Kano
- ‘Yan takara sun koka kan shirin zaɓen a Kaduna
- Da sauran lokaci — Masu zaɓe a Katsina
- Mayar da zaɓukan ƙarƙashin Hukumar INEC ne mafi ta — Buba Kwaccham
Yayin wasu jihohi suka gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi don cika umarnin Kotun Ƙoli, yanzu wasu na rigerige wajen yin zaɓen saboda rashin tabbacin samun kuɗaɗen shiga daga Gwamnatin Tarayya don cika wa’adin gama zaɓuka.
Alamu na nuna akwai danbarwa da da zargin hukumomin zaɓen jihohi da rashin yin kyakkyawan shiri kan zaɓukan.
Umarnin cewa jihohi su yi zaɓukan wani mataki ne na aiwatar da hukuncin da ta ba wa ƙananan hukomin Nijeriya ’yancin cin gashin kansu.
Babban ɗan siyasa kuma mai rajin kare haƙƙin al’umma, Alhaji Abdurrahman Buba Kwacham ya ce zai yi wuya gwamnoni su bar ƙananan hukumomi su samu ’yancin cin gashin kai kamar yadda kotun ƙoli ta yanke hukunci, matuƙar zaɓukan ƙananan hukumomi za su ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar gwamnonin.
Ya ce ’yancin zai yiwu ne kawai idan aka ɗauke ragamar zaɓen daga hannunsu a ka damƙa shi a ƙarƙashin wata hukumar zaɓe ta tarayya don kula da zaɓukan ko kuma mayar da shi a ƙarƙashin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
“Za a iya haɗa zaɓukan a rana guda don samar da sauƙi wajen gudanar da shi tare da sauran zaɓuka kamar na shugaban ƙasa da na gwamnoni da na ’yan majalisun tarayya da kuma jihohi. Sai kuma na ƙananan hukumomi da kansioli da suke aiki tare.
“Wannan shi ne nake ganin zai kawo sauƙi wajen maguɗi da kuma kama-karya. Kuma za sanya a bari ƙuri’ar jama’a ta yi aikinta sannan kuma ya kawo sauƙin kashe kuɗi wajen aiwatar da zaɓen saboda za a dunƙule shi lokaci guda,” in ji shi.
Alhaji Abdurrahman Kwaccham ya ce hukuncin da kotun ƙolin ta yanke na ba da damar cin gashin kai ga ƙananan hukumomi, idan a ka aiwatar da shi, tsari ne da zai kawo cigaba da kuma samar da sauƙi rayuwa ga yankunan karkara da kuma al’ummarsu.
“Ka duba ka ga yadda ƙananan hukumomi a yanzu suka koma kusan ba sa aikin komai banda biyan albashi na je-ka-na-yi-ka. Hakan ya saɓa da abin da aka sani a baya lokacin da ƙananan hukumomi ke dogaro da kansu, kuma suke gudananr da sabbin ayyuka da gyare-gyare a mataki irin nasu. Hakan ya samar da sauƙin rayuwa da kuma rage kwararar al’umma zuwa birane da ke kassara ayyukan noma,” in ji Kwaccham.
Ya ci gaba da cewa, ”sai dai an rasa dukkan wannan cigaba a halin yanzu, saboda yadda gwamnononi ke ɓarnata dukiyar da ya kamata ta je ƙananan hukumomi. A tsarin zaɓe da ake bi a yanzu zai yi wuya gwamnoni su bar al’umma su zaɓi waɗanda suke so, sannan koda an zaɓe su za su ci gaba da takura musu saboda tsarin zaɓen da ke kawo su yana ƙarƙashin kulawar gwamnonin ne sai yadda su ka yi da su”.
Shirye-shiryen zaɓen a Kaduna
A Jihar Kaduna shirye-shirye na ci gaba da gudana dangane da zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a ranar sha 19 ga watan nan da muke ciki.
Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa aƙalla jam’iyyun siyasa goma ne Hukumar Zaɓen Jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta tantance domin shiga zaɓen daga cikin jam’iyyu 19.
Ya zuwa yanzu duk ’yan takara suna ci gaba da yaƙin neman zaɓe ne ta hanyar bin gidaje da makarantun Islamiyya da inda suke tara matasa domin yaɗa manufofinsu.
Alamu na nuna cewa manyan jam’iyyun da za su fafata a jihar su ne jam’iyar mai mulki ta APC sai kuma PDP wacce ita ce babban jam’iyyar adawa. Bayan ita sai jam’iyar PRP da NNPP da kuma LP. Ya zuwa yanzu waɗannan ne kaɗai ake jin ɗuriyar ’yan takararsu.
A shirye muke mu shiga zaɓen- PDP
Aminiya ta zanta da Mariya Samuel Dogo Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta PDP a Jihar Kaduna, wacce ta bayyana cewa a shirye jam’iyarsu take domin shiga zaɓen.
Sai dai ta roƙi Hukumar Zaɓe da ta yi adalci a duk abin da za ta yi dangane da zaɓen inda ta ce ya kamata hukumar ta yi taka-tsantsan ka da ta zama ’yar amshin shatar gwamnatin jihar.
“Domin tun ba a yi nisa ba mun ji gwamna na faɗin cewa tun da ƙarfe sha biyun rana zai ambaci sakamakon zaɓen. Abin da muke faɗa shi ne muna buƙatar adalci daga hukumar KADSIECOM,” in ji ta
Ta ci gaba da cewa, “Ba mu jin tsoron wannan zaɓe, domin a shirye muke don tuni muka fara yaƙin neman ƙuri’a. Kuma ’yan takararmu a shirye suke. Kawai dai muna kira ne ga hukumar KAD-SIECOM ta yi abin da ya dace.”
Ta ƙara da cewa, tsohon Gwamna Nasir El-rufai ya kwatanta adalci a zaɓen ƙananan hukumomi a lokacin mulkinsa don haka sai ta shawarci Gwamna Uba Sani da ya tabbatar da an yi zaɓen adalci.
Ta kuma yi kira ga magoya bayan Jam’iyyar PDP da su tabbatar da sun saka idanu a sakamakon zaɓen don tabbatar da abin da suka zaɓa a akwatunan zabensu aka ba su a runfunan zaɓe da kafafen yaɗa labarai.
Sannan su guji yaɗa jita-jita a kafafen sada zumunta, wanda hakan zai taimaka wajen rage duk wani rashin gaskiya da za a nemi yi a zaɓen.
’Yan takara sun koka kan shirin zaben
Gamayyar ’yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi da kansaloli na jam’iyyin adawa a Jihar Kaduna, a wani taron manema labarai un koka kan rashin bin ka’idojin zaɓe da Hukumar Zaɓe ta jihar ke yi.
Shugabansu, Kwamrade Mohammed Hamisu Umar, ya ce, “Mun san abin da ake mana mun kuma duba doka mun ga ba daidai ba ne, saboda haka muna so a gyara sannan abi ka’idar abin da ya kamata.
“Ana yi wa doka karan-tsaye da ƙin bin ƙa’idojin ƙasa tun daga shugaban ƙasa zuwa gwamna zuwa sanata zuwa ɗan majalisar tarayya da na jihar. A fito a gaya mana wanda ya biya kwabo kafin ya zama abin da ya zama.
“Saboda haka ba a biyan kuɗi kuma doka ba ta ba da damar a saka mana kuɗin ba. Shi ya sa muka ce wannan dokokin da aka bi ba tsari ba ne. Daga ciki kuma aka ce wai sai ka nuna takardar biyan haraji na shekaru uku baya, kafin lokacin zaɓe wanda shi ma ya yi tsauri. Kuma ba ya cikin tsarin kundin zaɓe na ƙasa a shekarar 2022.
Jam’iyyu 10 muka tantance — KAD-SIECOM
Kakakin Hukumar KAD-SIECOM Farfesa Joseph Gambo ya ce, jam’iyu 10 ne aka tantance da za su fafata a zaɓe mai zuwa daga cikin jam’iyyu 19.
Ya kuma bayyana sunayensu kamar haka: Jam’iyyar APGA da APC da PDP da NNPP da PRP da LP da YPP da ADC da ZLP sai kuma Jam’iyyar AA.
Ya ƙara da cewa, “akwai ’yan takarar kujerar shugaban ƙananan hukumomi 79 da aka tantance za su don yin takara a zaɓe mai zuwa daga cikin waɗannan jam’iyyu goma.
“Jadawalin da hukumar ta fitar a watan Yulin shekarar nan dangane da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar ya nuna cewa za a yi zaɓen ne a ranar 19 ga watan Octoba. Saboda haka kamar yadda muke bin wannan jadawali ba tare da wata matsala ba,” in ji shi.
Farfesa Joseph, ya kuma ba da tabbacin cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ta yi adalci a zaɓen.
Cikakken rahoton a nemi Jaridar AMINIYA.
Daga Adam Umar, Abuja da Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna da Musa Kutama, Kalaba da Salim Umar Ibrahim, Kano da Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina