✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Anambra: An fara kada kuri’a a Ihiala

Za mu kawo muku yadda take wakana kai tsaye a zaben.

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanya Talata a matsayin ranar da za a kammala zaben Gwamnan Jihar Anambra.

Hukumar dai ta ayyana zaben na ranar Asabar a matsayin wanda bai kammala ba, har sai an sake yi a mazabu 320 na Karamar Hukumar Ihiala.

Tuni dai aka fara kada kuri’a a Karamar Hukumar wacce ke da masu zabe 148,407.

Ku kasance tare da mu a shafinmu na intanet da shafukanmu na sada zumunta na Facebook da Twitter da Instagram don jin yadda take kayawa.