Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanya Talata a matsayin ranar da za a kammala zaben Gwamnan Jihar Anambra.
Hukumar dai ta ayyana zaben na ranar Asabar a matsayin wanda bai kammala ba, har sai an sake yi a mazabu 320 na Karamar Hukumar Ihiala.
- Muhimman abubuwa 8 da suka faru a Kannywood cikin makon nan
- Za a debi matasa 10,000 aikin gadin bututan mai a Kogi
Tuni dai aka fara kada kuri’a a Karamar Hukumar wacce ke da masu zabe 148,407.
Ku kasance tare da mu a shafinmu na intanet da shafukanmu na sada zumunta na Facebook da Twitter da Instagram don jin yadda take kayawa.