Dan takatar Shugaban Kasar Amurka a jam’iyyar Democrat, Joe Biden ya ce kiran da Shugaba Donald Trump ke yi da a dakatar da kirga kuri’un da aka kada a zaben ya saba tunani.
Biden ya kara da cewa kiran na Trump mai neman wa’adin mulki na biyu a zaben, abu ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar kuma yunkuri ne na tauye hakkin Amurkawa; kuma a shirye lauyoyinsa suke su dakile yunkurin
- Zaben Amurka: Na lashe zabe amma zan garzaya kotu —Trump
- Ce-ce-ku-ce hudu da Rahama Sadau ta jawo a Kannywood
A wani jawabi da ya yi da talatainin daren Laraba, Trump ya nemi a dakatar da kirga kuri’un yana mai cewa zai garzaya zuwa Kotun Koli bayan ya yi ikirarin cewa ya lashe zabe.
Bayan jawabin nasa kungiyar yakin neman zaben Biden ta mayar masa da martani da cewa, “Jawabin Shugaban Kasa na kokarin tsayar da kirga halastattun kuri’un da aka jefa wuce makadi da rawa ne, ba a taba yin haka ba kuma kuskure ne”.
Bayanin manajan yakin neman zaben Biden, Jen, O’Malley Dillon ya ci gaba da cewa bayanin Trump, “Ya wuce haddi saboda yunkuri ne a bayyane na kwace ’yancin Amurkawa.
“Ba a taba yin haka ba a tarihinmu inda shugaban kasa ke neman toshe muryar ’yan kasa a zaben kasa”.