✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2024: Trump ya daukaka kara a Kotun Koli

Jihar Colorado ita ce ta farko da ta yanke hukuncin haramta wa Trump.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya daukaka kara zuwa kotun koli kan hukuncin kotun Jihar Colorado da ta haramta masa tsayawa takara a zaben 2024.

Jihar Colorado ita ce ta farko da ta yanke hukuncin haramta wa Trump takara bisa tuhumarsa da tunzura afka wa majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun 2021.

Trump wanda ke kan gaba a cikin ‘yan takarar neman shugabancin kasar Amurka na 2024 a Jam’iyyar republican yana bukatar kotun kolin ta sake duba hukuncin.

Manazarta dai na ganin karar za ta jefa kotun kolin cikin wadi mai sarkakakiya na siyasa.

Uku daga cikin alkalan kotun dai Trump ne ya nada su a lokacin da ya ke shugaban kasa.