Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya yi alkawarin cewa babban zaben 2023 zai fi kowanne zabe da Najeriya ta taba yi a tarihi.
Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata, yayin da yake karbar wakilan jami’ar IRI da na makarantar NDI na kasar Amurka.
- An tsinci gawar malamin cocin da ’yan bindiga suka sace a Kaduna
- Cutar Kwalara ta kashe mutum 5 a Kano
Ya ce taron shi ne irinsa na farko da INEC din ta jagoranta tun bayan gudanar da zaben Gwamnan jihar Osun, tare da tabbatar da cewar hukumar za ta ci gaba da samun nasara a zabuka na gaba.
Ya ce, “Muna tabbatar muku cewa za mu ci gaba da jajircewa domin ganin zaben 2023 ya yi daidai da abin da al’umma ke so.
“An ga dai yadda muka cika alkawarin yin ingantaccen zabe a Ekiti da Osun, to wannan alkawarin ma makamancinsa ne da zan bugi kirji na ce sai ya fi duk wanda aka taba yi a baya inganci.
A nasa bangaren, Sakataren Kasa na jihar Ohio da ke Amurka, wanda shi ma Kwamishinan Zabe ne a can, Frank LaRose, ya yaba wa INEC kan kokarinta na inganta tsarin zabe a Najeriya.
Ya kuma kwatanta wannan ziyara tasa ta farko zuwa Najeriya a matsayin babbar damar daukar darussa daban-daban.
Ya kuma karfafa wa INEC din guiwar dorawa kan kokarin da take wajen inganta zabukan kasar.
“Na jagoranci tawagar kwararru na musamman a harkar zabe daga Najeriya da Amurka, kuma mun zagaya cibiyoyin zabe da dama domin ganewa idanunmu yadda aka gudanar da zaben karkashin sabuwar dokar zaben, ina mai tabbatar muku cewa an sami ci gaba sosai a zabukan Najeriya,” inji shi.