✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben 2023: Zabi ya rage ga talakawan Gombe

Mu dai masu zabe yanzu sai yadda muka ce, domin zabin namu ne.

Yanzu da aka kammala zaben fid-da-’yan takara a Jihar Gombe, hankali ya koma kan manyan jam’iyyun APC da PDP.

Manyan ’yan takarar su ne, Gwamnan Jihar Gombe na yanzu, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya na APC da Alhaji Jibrin Danbarde na PDP. Mu dai masu zabe yanzu sai yadda muka ce, domin zabin namu ne.

Da farko, wadansu suna ganin babu wani tasiri da dan takarar PDP zai yi musamman ganin cewa wadansu ba su san shi ba, sai dai nasarar Alhaji Atiku Abubukar wanda dan yankinsa na Arewa maso Gabas ne, ya sa wadansu na tunanin zai iya yin tasiri domin tasirin Atikun.

Haka shi ma Gwamna mai ci, rikicin cikin gida da ya kusa cin jam’iyyar a kusan shekara uku ya so ya kawo masa cikas, inda aka ta yin rikici tsakaninsa da tsohon Gwamna Danjuma Goje wanda maigidansa ne kafin daga bisani su yi sulhu.

Wannan ya sa masu sharhi a kan siyasar Jihar Gombe suke ganin wannan fafatawar sai dai kawai a ce ba a san maci tuwo ba, sai miyar ta kare. Ke nan sai yadda mu talakawa masu zabe muka yi da su domin filin dagar a bude yake.

Sai dai idan aka yi la’akari da tarihin baya, za a iya cewa irin wannan rikicin ya sha faruwa tsakanin Goje da yaransa, wanda a lokuta da dama yake jawo sabani mai karfi.

Ke nan idan har ta ido kawai aka yi a wajen sulhun, za a iya cewa akwai sauran rina a kaba, musamman idan aka tuna rikicin da aka yi lokacin da Sanata Goje ya zo shigo Gombe a Nuwamban bara, inda aka fatata da masoyansa, rikicin da aka yi zargi magoya bayan Gwamna Inuwa da shiryawa, su kuma suka zargi bangaren Sanata Goje.

Daga cikin abubuwan da aka yi amfani da su wajen yaki da tsohon Gwamna Dankwambo shi ne zargin bai taimaki wadansu da suka yi masa kokari ba da kuma rashin kokari wajen yaki da talauci, amma a maganar ayyukan raya kasa, ana tunanin ko Sanata Goje bai fi Dankwambo ba.

Gwamna Inuwa Yahaya yana kawo uzuri da tabarbarewar tattalin arzkin kasa, wanda ba ma Najeriya ba, duniya ma ta shiga, wajen rashin samun cika wasu alkawuran da ya dauka. Sai dai matsalar ita ce, su masu zabe ba su san wannan ba.

Masu zabe babu ruwansu da bayani, cewa za su yi “To ba donwannan muka zabe ka ba?”

Babban abin da ya kamata Gwamna Inuwa ya yi shi ne gyara wasu tsare-tsarensa, musamman wadanda mutane ba sa jin dadinsu domin ya dadada musu, sai dai da wahala ganin yanzu bai wuce saura wata bakwai a gabansa ba kafin zabe. Wani abin da zai taimaki

Gwamna Inuwa shi ne nasarar Alhaji Danbarde, domin mutane sun fi sanin Jamilu Gwamna a ’yan PDP na jihar.

Sai dai nasarar Atiku Abubakar za ta iya taimakon Danbarden shi ma, sannan idan suka hada karfi da karfe da Jamilu Gwamna, wanda shi ne ko’odinatan Atiku a Arewa maso Gabas, za su kawo wa Gwamna Inuwa tarnaki.

Dokta Jamilu Gwamna yana da masoya da dama saboda yadda ya yi kokarin dadada musu, shi ya sa suka so a ce shi ne dan takarar PDP, idan suka hada kai da Barde, za su ba Inuwa Yahaya wahala duk da karfin gwamnati da ke hannunsa.

Sai dai wadansu na ganin dan takarar PDP din a matsayin bai yi fice ba, amma kuma mutum ne da ya kware wajen bin mutane.

Kusan shekara daya ya yi yana bibbiyar mutane musamman a PDP din, wanda hakan ya sa cikin ruwan sanyi ya tara masoya a cikin masu ruwa-da-tsakin jam’iyyar, wanda hakan ya sa ya lashe zaben fid-da-gwanin.

Akwai kuma sauya sheka da wasu jiga-jigan APC suka yi, wanda shi ma kalubale ne babba ga Gwamna Inuwa. Sai dai duk da haka, Gwamna Yahaya yana da uban siyasar Gombe Sanata Goje da kuma mulki a hannunsa.

Yanzu abin da ya rage shi ne ko Gwamna Yahaya zai iya tsallake siradin da ke gabansa ya doke Alhaji Danbarde?

Ko kuma Danbarde ne zai masa ba-zata ya doke shi?

Mu dai talakawa zabin namu ne. Ina kira mu tantance mu dubai abin da ya fi dacewa da jiharmu.

Umar Alkalam Sule, umara[email protected] Ya rubuto wannan makala ce daga Akko, Jihar Gombe.