Gwamnatin Birtaniya ta ce a shirye take ta dauki matakin kan wadanda ke shirin yi wa tsarin dimokuradiyya karan tsaye a zabubbuka masu zuwa a Najeriya.
Cikin sanarwar da ofishin jakadancinta a Najeriya ya fitar ranar Talata a Abuja, Birtaniya ta ce za ta zuba ido kan yadda zaben Najeriya zai gudana a Fabrairu da Maris, 2023.
- Tsoffin kudi: Masu kuste sun yi mini lalata —Aisha Buhari
- Mahara sun kona sakatariyar karamar hukuma a Kogi
“Inda Birtaniya ta sani cewa ana shirin murkushe tsarin dimokuradiyya, walau a matakin kasa ko jiha, a shirye muke mu dauki mataki kan masu haddasa rikicin zabe da makamantansu.
“Matakin ka iya hadawa da hana mutane bizar Birtaniya ko saka takunkumi kan wasu ’yancin bil Adama,” Kamar yadda Jakadan Birtaniya a Najeriya, Andrew Mitchell, ta bayyana.
Mitchell ta ce, Gwamnatin Birtaniya ta jaddada aniyarta ta mara wa Najeriya baya domin tabbatar da nagartar zabe mai karatowa.
“Najeriya kasa ce mai muhimmannci ga Birtaniya, don haka za ta sa ido sosai a zaben Shugaban Kasa da na gwamnoni da na ’yan majalisun tarayya da za a gudanar nan da ’yan kwanaki,” in ji Mitchell.