✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben 2023: Za a fara tantance ’yan takarar PDP

PDP za ta fara tantance ’yan takara 17 da suke neman kujerar shugaban kasa.

A ranar Juma’a ce Jam’iyyar PDP za ta fara tantance ’yan takara 17 da suke neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin inuwarta a zaben 2023.

Wadanda za a tantance sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal.

Haka aikin tantancewar zai hada da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.

Sai kuma mashahurin mai masana’antun nan, Mazi Sam Ohuabunwa da tsohon fitaccen ma’aikacin bankin nan, Mohammed Hayatu-Deen da kuma wani likita a Amurka, Nwachukwu Anakwenze da mawallafin Mujallar Ovation Dele Momodu.

Har ila yau akwai tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose da Mista Cosmos Ndukwe da Mista Charles Ugwu da Chikwendu Kalu da kuma Tariele Diana Oliver.

A cikin jadawalin da Sakataren Jam’iyyar PDP na Kasa Umar Bature ya fitar ya bayyana cewa za a gudanar da taron tantancewar ne a Legacy House da ke Abuja.

Kuma aikin tantancewar ya shafi duk masu neman takarar kujerar gwamnoni da na majalisun jihohi da na tarayya, daga jihohi bakwai na shiyyar Arewa maso Yamma da suka hada da Sakkwato da Kano da Kaduna da Katsina da Jigawa, Kebbi da Zamfara, wanda aka gudanar a shekaranjiya Laraba da jiya Alhamis.

Za a kuma gudanar da tantance masu neman sauran muqamai a sauran jihohin da suka rage a sakatariyar jam’iyyar, in ban da Jihar Anambra, da za a gudanar a sakatariyar jam’iyyar na shiyyar.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata David Mark, shi ne Shugaban Kwamitin mutum tara da za su tantance wadanda za su tsaya takarar Shugaban Kasar.

Sauran mambobin kwamitin sun haxa da Cif Celestine Omehia da Cif Mike Ahamba (SAN) da Dokta Olusegun Mimiko da Edward Ashiekaa (SAN) da Misis Hilda Makonto.

Sauran su ne da Dokta Aqilu Indabawa da Hajiya Hassana Dikko da Dokta Esther Uduehi, yayin da Madam Chinedu Nwachukwu za ta kasance a matsayin sakatariyar kwamitin.