A daidai lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ke shirin kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu, ’yan takarar da suke neman maye gurbinsa da suke takara a jam’iyyu daban-daban sun fara daukar harama.
A ranar 28 ga wannan wata ne ake sa ran dage takunkumin fara yakin neman zabe, inda ’yan takarar za su fara zagayawa domin neman kuri’un mutanen jihar don shiga Gidan Sa Kashim domin jan ragamar mulkin jihar.
Tuni jam’iyyun suka tsayar da ’yan takarar da suka fara tuntuba tun kafin isowar ranar 28 ga Satumban da Hukumar INEC ta sa domin fara kamfe.
Aminiya ta yi tankade da rairayi kan kalubale da kuma abubuwan da kowane dan takara zai iya tinkaho da su don ganin ya lashe zaben mai zuwa.
Masana harkokin siyasa a jihar na ganin zaben Gwamnan zai kasance ne a tsakanin jam’iyyu biyar duk da kasancewar akwai jam’iyyu 18 da ka iya tsayawa takara a zaben kasa baki daya, sai dai akasarinsu ba su da ’yan takara in kuma akwai, ba su yi fice ba.
’Yan takara biyar da suka fi motsawa a jihar dangane da takarar Gwamnan su ne Sanata Suleiman Othman Hunkuyi da ke takara a Jam’iyyar NNPP.
Sai Mista Jonathan Asake, tsohon Shugaban Kungiyar Mutanen Kudancin Kaduna (SOKAPU) da ke takara a Jam’iyyar Labour (LP) sai Malam Hayatuddeen Lawal Makarfi da ke takara a Jam’iyyar PRP.
Sai tsohon dan Majalisar Wakilai, Alhaji Isa Mohammed Ashiru na Jam’iyyar PDP, sai kuma Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Malam Uba Sani na Jam’iyyar APC.
Aminiya ta yi kokarin auna nauyin kowanensu a sikeli tare da yin nazarin yadda siyasar za ta kasance.
A siyasar Jihar Kaduna, akwai yankin Zariya da akasari Hausawa da Fulani ne, sai tsakiyar jihar da yawanci ake yi lakabi da ka-zo-na-zo, sai yankin Kudancin jihar da mafi yawansu kabilu ne.
Hayatuddeen Makarfi
Dan siyasa ne kuma matashi mai kokarin ba da gudunmawa wajen ci gaban jihar. Sai dai akwai wadanda suke ganin ba sananne ba ne a siyasar jihar kuma duk da kasancewar Jam’iyyar PRP ta kwashe kusan shekara 50 ana damawa da ita a siyasar kasar nan, mutane da dama na ganin kila a wannan karon ta tabuka abin a zo-a-gani.
Sai dai akwai bukatar ya motsa a lokacin yakin neman zabe wajen tallata kansa da manufofinsa, musamman ganin ana bukatar kudi mai yawa da za a tallata dan takara a yankuna uku na jihar.
Sanata Suleiman Othman Hunkuyi
Fitaccen dan siyasa ne a Jihar Kaduna da aka dade ana damawa da shi domin ba wannan ne karo na farko da yake takarar Gwamnan ba a jihar, inda tun daga shekarar 2003 yake takara.
Ana yi masa kallon dan siyasa kwararre kuma mara tsoro musamman ganin yadda ya kasance cikin wadanda suka rika kalubalantar wasu daga cikin manufofin Gwamna El-Rufa’i lokacin yana Sanata.
Sanata Hunkuyi sananne ne a fadin jihar, wanda hakan ke nufin rage nauyin tallata dan takarar, sannan ganin ya taba yin Sanata, wannan wata madogara ce.
Sai dai ko sunansa zai taimaka masa wajen cin zabe a sabuwar Jam’iyyar NNPP?
Wannan wani abu ne daban kasancewar Jam’iyyar NNPP sabuwa ce duk da cewa ta samu karbuwa musamman a Jihar Kano da ke da makwabtaka da Kaduna.
Jonathan Asake Jonathan
Asake na Jama’iyar Labour shi ma sananne a yankin Kudancin Kaduna kasancewar ya Shugabanci Kungiyar SOKAPU.
Sai dai jam’iyyarsa ta Labour Party ba sananniya ba ce a jihar, duk da ta kasance tsohuwa kuma tana da karfi a yankin Ibo.
Ana ganin Asake zai samu kuri’u a yankinsa, sai dai tambayar a nan ita ce kuri’un Kudancin Kaduna kadai sun isa sa ya lashe zaben Gwamna?
Sannan ga kasancewar yankinsa ne Jam’iyyar PDP ta fi karfi a jihar.
Isa Ashiru
Alhaji Ashiru Isa Kudan, dan takarar Jam’iyyar PDP kuma tsohon dan Majalisar Wakilai takararsa ta uku ke nan.
Ya fito takarar a shekarar 2015 da 2019 sai kuma zaben badi 2022.
Masana harkokin siyasar jihar na ganin PDP na da damar tabukawa sosai a zaben na badi bayan APC ta kwashe shekara kusan 8 tana mulki a jihar.
Wasu na ganin daga cikin abubuwan da za su taimaki jam’iyyar akwai batun da ake tunanin akwai mutanen jihar da dama da suka yi fushi da jam’iyyar da wasu daga cikin shugabanninta.
Wannan ya sa wasu suke ganin kila wasu mutanen su huce haushinsu a kan jam’iyar ta APC da dan takararta.
Ana amfani da zaben shugabannin kananan hukumomin da ya gabata a matsayin misali cewa akwai alamar watakila mutane sun fara gajiya da APC a jihar, inda PDP ta samu nasarar a wasu wuraren.
Haka kuma kasancewarsa a Jam’iyyar PDP, wadda babbar jam’iyya ce sananniya da ke rike da wasu kujeru da kuma kasancewarsa tsohon dan siyasa, ba zai sha wahalar tallata kansa ba.
Sai dai jam’iyyar ta PDP wasu na ganin tana da jan aiki a gabanta saboda yankin da take alfahari da shi wato Kudancin Kaduna na cikin rudani, kasancewar dan yankin ya fito takara a Jam’iyyar Labour.
Sannan dan takarar fitacce ne kasancewar alakarsa da fafutikar da ya yi a Kungiyar SOKAPU, inda ake tunanin zai iya rabawa ko lalata kuri’un da za su fito daga yankin, kuma hakan na iya shafar nasarar Ashiru Kudan a zaben mai zuwa.
Haka kuma akwai rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar, inda akwai masu ganin cewa tilas ne ya dage wajen neman sulhu da wasu jiga-jigan jam’iyyar a jihar domin samun goyon bayansu sannan akwai bukatar bayyana manufofinsa da na jam’iyarsa duk da cewa PDP ba sabuwar jam’iyya ba ce a jihar da kasa baki daya.
Sanata Uba Sani
Sanata Uba Sani, dan takarar Jam’iyyar APC ana ganin zai tabuka sosai saboda kasancewarsa dan jam’iyya mai rike da mulkin jihar.
Haka kuma gogagen dan siyasa ne da ya dade a fage, inda tun a zamanin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya rike Mashawarcin Shugaban Kasa.
Hakan ya sa wasu ke tunanin akwai karfin jam’iyyar mai mulki da kuma kasancewarsa Sanata mai ci da za su iya taimaka masa.
Sai dai wasu na ganin wasu daga cikin ayyukan Gwamna Nasiru El-Rufa’i musamman a bangaren ma’aikata da sabunta biranen jihar da a lokuta da dama suka fusata mutane, za su iya kawo tarnaki ga dan takarar.
Haka kuma akwai rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaben fidda-gwanin APC, inda wasu suke ganin ba a yi musu daidai ba kuma har yanzu ba su hakura ba.
A yanzu haka Alhaji Sani Sha’aban wanda ya shigar da kara a kotu kan zaben fitar da gwanin da aka yi, wanda wannan ma ba karamin tarnaki ba ne a gabansa.
A yanzu dai wuka da nama duk suna hannun masu zabe ne domin su ne suke da hurumin zabar wanda suke so ya shugabance su a zabe mai zuwa.
Sannan a daidai lokacin da ’yan takarar suke shirin fara yakin neman zabe, su kuma masu zaben suke ta auna ’yan takarar, da wannan za a iya cewa ba a sanin maci tuwo, sai miya ta kare.