✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben 2023: Watakila mace ta gaje ni – El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai, ya ce mace ce zata iya zama wacce  zata gaje shi a matsayin Gwamnan jihar a zaben 2023. Gwamnan ya…

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai, ya ce mace ce zata iya zama wacce  zata gaje shi a matsayin Gwamnan jihar a zaben 2023.

Gwamnan ya ce a yayin da wasu ke tunanin ya fitar da dan takara wanda zai gaje shi, zai iya zabar mace a matsayin wacce zai zaba kamar yadda ya zabi Mataimakiyarsa mace, Hadiza Balarabe a matsayin Mataimakiyar Gwamna.

Gwamna El-rufai, ya kara da cewa, lokaci bai yi ba da zai fara tunanin zaben shekarar 2023. Allah ne kadai Ya san wanda zai gaje shi a matsayin Gwamnan Kaduna.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau kafar rediyo lokacin da yake amsa tambayoyin masu saurarensa. Sannan ya ce a yanzu haka akwai mutum 10 da ke da sha’awar neman takarar Gwamnan jihar.