✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Fostocin Tinubu sun mamaye birnin Abuja

Fastocin sun bayyana a wurare da dama a babban birnin kasar.

Fostocin yakin neman zaben Jagoran Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun bayyana a wurare da dama a babban birnin kasar, Abuja.

An shaida ganin fostocin Tinubu, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas ne a ranar Lahadi wanda hakan ke nuna zai tsaya takarar Shugabancin Kasa a zaben 2023 da ke tafe.

Fostocin da ke dauke da hoton Tinubun an lika su ne a turakun lantarki da allunan bai wa motoci damar wucewa a hanya da dai sauran wurare a unguwannin Wuse II da Garki da ma Sakatariyar Jam’iyyar ta APC da ke daura da Ma’aikatar Shari’a a Babban Birnin Tarayyar.

Wasu daga cikin fastocin suna dauke ne da rubutu kamar haka: ‘Barka da Ranar Dimukoradiyya’, da ‘Kungiyar Masu Rajin Tinubu a 2023.’

Kungiyoyi da dama ne dai suka bayyana wajen nuna goyon bayan Tinubu ya tsaya takara gabanin zaben 2023.

A kwanakin baya, wata kungiya da ake kira SWAGA 2023, ta rika kai komo a tsakanin Jihohin yankin Kudu maso Yamma, tana mai kiran da a mara wa Tinubun baya, duk da cewa har yanzu bai riga ya fito ya shelanta aniyarsa ta tsaya wa takarar ba.

Har wa yau, an kuma bude ofishin gangamin neman zaben Tinubu a unguwar nan ta attajirai Maitama a Abuja, inda a nan ne kungiyoyin da ke rajin tsaya wa takararsa ke gudanar da harkokinsu.