✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben 2023: Amurka ta ware Dala miliyan 50 na gudunmawa ga Najeriya

Amurka ta kuma ce za ta tabbatar an yi adalci a zaben

Kasar Amurka ta ware Dala miliyan 50 a matsayin gudunmawarta ga Najeriya a babban zaben da za ta gudanar a shekarar 2023 mai zuwa.

Hakan ya fito ne daga bakin Jakadan Amurkar a Najeriya, Mista Will Stevens a jawabin da ya gabatar yayin wani taron horar da ’yan jarida wanda Cibiyar Horas da ’Yan jarida Afrika ta Yamma (WABMA)  ta shirya a Ibadan a ranar Litinin.

Jakadan ya kuma ce gwamnatin Amurka na aiki tukuru da aminanta ta hannun Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa (USAID), domin ganin an yi adalci a zaben.

Daga cikin abubuwan da za a yi da kudaden da kasar za ta bayar har da horar da ’yan jarida kan aikinsu da kungiyoyin fararen hula.

Sannan kuma za a taimaka wajen samar da kayayyakin aiki domin tabbatar da ingantaccen zabe.