Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce a shirye ta ke wajen samar da tsaron da ake bukata a lokacin zaben Shugaban Kasa da za a gudanar a jihar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Mamman Dauda ne ya bayar da wannan tabbacin lokacin da yake zanta wa da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Kano a ranar Litinin.
- APC ta bukaci Buhari ya mutunta umarnin Kotun Koli kan wa’adin tsofaffin kudi
- Ba mu kai samame gidan Tinubu ba —EFCC
Dauda, ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar suna bakin kokarinsu wajen ganin an gudanar da zabe ba tare da rikici ba a dukkan sassan jihar.
Ya bayyana cewa, tuni aka bayar da umarnin yadda yadda za a samar da tsaro a kowace rumfar zabe da ke fadin kananan hukumomi 44.
“An yi wa kwamandoji da jami’an ‘yan sanda na yanki cikakken bayani kan matakan tsaro daban-daban da za a dauka domin tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana.
“Mun tanadi isassun jami’an tsaro domin samar da tsaro kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe,” in ji kwamishinan.
“Ina ba da tabbacin kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda, cewa za su iya tafiya cikin walwala don yin zabe a ranar 25 ga Fabrairu ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji shi.
Dauda ya bayyana cewa matakan tsaro da aka sanya za su bai wa wadanda suka cancanci kada kuri’a damar shiga dukkan rumfunan zabe ba tare da wata barazana ba.
“Mun samar da hanyoyin tsaro daban-daban don bai wa mazauna jihar nan damar samun zabar shugabannin da suke so cikin lumana,” in ji shi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su ja hankalin magoya bayansu da su guji duk wani nau’in tashin hankali kafin zabe da lokacin da kuma bayan zabe.
Ya ce duk wasu gungun mutanen da aka samu suna kokarin tayar da tarzoma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
“Za mu samar da yanayi mai kyau ga dukkan jam’iyyun siyasa don gudanar da zabe yadda ya kamata yayin da ake aiwatar da shirin mika mulki.
“Ba za mu amince da duk wani yanayi da zai iya kawo rudani kafin zabe, lokacin zabe da kuma bayan zabe ba; duk wani mutum ko kungiyoyin da aka samu sun ki bin umarni za a kama su kuma a gurfanar da su a gaban kuliya.”
Kwamishinan ya yi kira ga iyaye da kada su bari a yi amfani da ’ya’yansu wajen bangar siyasa domin hukuma ta yi tanadi mai tsauri ga wanda ya shiga hannunta.