Na Abdullahi bin Muhammad bin Abdul’Aziz bin Humaid
Fassarar Imam Ahmad Adam Kutubi
Gabatarwa:
Duk da cewa maniyyata aikin Hajjin bana na daf da fara tashi, muna ganin ba mu makarab ba, idan muka gabatar da wani abu kan wannan rukuni na Musulunci mai girma. Imama Ahmad Adam Kutubi ne ya aiko mana da wannan rubutu wanda ya fassara daga littafin Shehin Malami Abdullahi bin Muhammad bin Abdul’aziz Humaid daya daga cikin limaman Ka’aba:
Tambaya: Shin wajibi ne ga mai iko duk shekara sai ya yi aikin Hajji? Ko kuwa sau daya ne yake wajibi?
Amsa: Ba dole ba ne sai an yi duk shekara, na wajibi sau daya ne a rayuwa. Koda kuwa mutum yana da iko, baya zama dole a kansa, kamar yadda ya zo a cikin Hadisai da dama cewa Manzon Allah (SAW) ya tara. Mutane ya yi musu Huduba ya kwadaitar da su kan aikin Hajji, sai wani Sahabi mai suna Akara’u dan Habis ya mike ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin duk shekara sai an yi? Sai ya ce: “A’a da na ce eh da sai ya zama wajibi, sau daya ake aikin Hajji.”
Tambaya: Wanda ya zo don yin Umara shin dole ne sai ya yi Hajjin wannan Shekara? Saboda muna jin Mutane suna fadar hakan shin gaske ne?
Amsa: Wannan kuskure ne, babu wanda ya fadi hakan cikin Malaman Musulunci.
Tambaya: Shin ya halatta ga yaran da ba su kai shekara bakwai ba su yi dawafi tare da mahaifansu?
Amsa: Ya halatta su yi haramar Hajji ko ta Umara, ko da ba su kai shekaru bakwai ba, kamar yadda ya zo a kissar matar nan Khas’imiyya wacce ta dauko karamin yaro da ke cikin tsumman goyo ta ce: “Ya Ma’iakin Allah! Shin wannan zai iya yin Hajji? Ya ce: “kwarai kuwa amma ladan naki ne.” Ta nan aka gane cewa Umarar yaron da bai kai shekaru bakwai ba ta halatta, kuma ya iya yin Hajji da dawafi amma a matsayin nafila.
Tambaya: Mace ce take da ’ya’ya ’yan shekaru tara zuwa ashirin, kuma tana da miji ya yi Hajji, amma ita ba ta yi ba, tana kuma da da balagagge, shin Hajji ya hau kanta?
Amsa: Na’am idan tana da iko, tana da dukiya za ta iya zuwa Makka ta dawo ba tare da bashi ba, ba tare da rokon mutane ba, Hajji ya wajaba a kanta a kowane hali, danta zai iyi tafiya da ita Hajjin, amma idan talaka ce Hajji bai hau kanta ba, saboda Allah (SWT) Yana cewa: “Allah Ya wajabta aikin Hajja a kan mutane ga wanda ya samu iko.” (Ali Imran: 97). Iko shi ne guzuri da abin hawa, a zamanin yanzu kuma guziri da kudin jirgi, idan kuma ba ta da komai to Allah ba Ya dora wa mutum abin da ba zai iya ba, wannan ana magana ne a kan Hajji na farillah, (balle na nafila).
Tambaya: Shin wajibi ne sai miji ya yi Hajji ko Umara da matarsa?
Amsa: Ya kamata ya yi Hajji da ita, ya kyautata mata amma babu batun dole, ba dole ne sai ya yi Hajji ko Umara da ita ba, kawai dai kyautatawa ce daga gare shi, ya kamata ya yi hakan, amma idan bai yi ba, ba ya da wani laifi.
Tambaya: Mene ne hukuncin wanda ya yi Hajji ko Umara ta hanyar kudin giya, saboda ba ya da wasu?
Amsa: Abu ne sananne cewa Annabi (SAW) ya yi bayani a kan wannan tamabayar inda yake cewa: “Hakika Allah idan ya haramta abu sai ya haramta cin kudinsa.” Shin giya haramun ce? Amsar ita ce ‘Eh’ babu tantama cewar haramun ce. Sai mu ce matukar dai haramun ce, to kudinta ma haramun ne saboda Annabi (SAW) yana cewa “Allah idan Ya haramta abu sai ya haramta kudinsa” don haka cin kudin giya ko amfani da su bai halatta ba, kamar yadda mushe yake haram bai halatta a yi amfani da nama ko kitsansa ba.
A takaice: cin kudin giya haramun ne, idan hakan ta faru dole ka tuba ka yi istigfari, idan ka yi tuba na gaskiya ana sa ran Allah zai yi maka afuwa Ya gafarta maka, shi kuwa tuba yana da sharudda uku:
– Na farko: Yin Nadama kan abin da aka aikata.
– Na Biyu: Ka kudurce cewa ba za ka kuma sake yi ba.
– Na Uku: Ka yi bakin ciki kan abin da ka aikata, ka kuma nisanci aikata makamantansa.
Tambaya: Ni ma’aikacin gwamnati ne, amma tsawon shekara ashirin ban yi aikin Hajji ba, yanzu kuma aiki ya yi min yawa ba zai yiwu in bar wajen aikina ba, shin zan iya wakilta wani ya yi min aikin Hajji?
Amsa: Matukar dai kana da karfi kuma za ka iya yin aikin Hajji, kamata ya yi ka nemi izini daga wajen shugabanninka, ka fada musu cewa har yanzu ba ka yi Hajjin wajibi ba, babu shakka za su ba ka dama sai su sa wani ya kula da aikinka. Saboda Hajjin wajibi dole ne ga mai iko, don haka bai halatta ka aiki wani ya yi maka ba, bayan kana da ikon yi.
Tambaya: Ina daukar nauyin Hajjin mahaifana daga garin Riyad duk shekara ina kashe sama da Riyal dubu uku don a yi musu Hajji. Sai na samu wani mutum a Makka zai yi musu Hajji da Umara a Riyal dubu biyu, shin hakan ya halatta kuma wane ne ya fi?
Amsa: Idan a Riyad din ka samu mutumin kirki mai tsoron Allah da zai yi cikakken Hajji, ina gani kamar zai fi saboda abin da aka fi bukata shi ne mutumin kirki nagari, ya karbi abin da yake ganin zai ishe shi
har ya gama aikin Hajjinsa, ina ganin babu laifi, kuma Allah zai karba ya ba ka lada.
Tambaya: Na yi aikin Hajjina kafin in balaga bayan kuma na balaga sai na yi wa wasu Hajji har sau biyu a jere, shin Hajjin da na yi musu ya yi, tare da cewa na yi nawa ne kafin in balaga?
Amsa: Hajjinka da ka yi kafin ka balaga wannan nafila ne, wanda kuma bayan ka balaga ka yi wa mutum biyu to, ba ta yi ba, sai dai in nasu na farko ya zama naka kamar yadda yake a Mazhabar Hambaliyya da wasunsu cewa: Idan Mutum ya yi wa wani Hajji kafin ya yi wa kansa, to yana mazaunin nasa; koda kuwa ya yi niyyar yi wa wancan din. Don haka na farkon naka ne kai kanka, na biyu kuma na wanda ka yi niyyar yi wa ne. Ya zo a kissar Sahabin nan mai suna Shubramata cewa: “Annabi (SAW) ya ji wani mutum yana cewa “AmsawarKa wannan Hajjin Shubramarata ne!” Annabi (SAW) ya ce: “Waye Shubramata?” Ya ce dan uwana ne.” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Shin kai ka yi wa kanka Hajjin ne?” Ya ce: “A’a,” Annabi (SAW)
ya ce : “Ka fara yi wa kanka Hajjin tukuna, sannan ka yi wa Shubramata.” Duk da cewa lokacin da zai yi harama ya yi ne da niyyar dan uwansa, amma Annabi (SAW). bai ce ya sake harama ba, sai ya sa shi
kawai ya canja niyya. Malamai suka ce wannan yana nuna idan mutum ya yi wa wani Hajji bayan shi bai yi ba, to nasa ne.