✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ƙwance Jihar Ribas a 2027 —Ganduje

Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya yi alƙawarin karɓe mulkin Jihar Ribas daga hannun PDP a zaɓen shekarar 2027.

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya yi alƙawarin karɓe mulkin Jihar Ribas daga hannun PDP a zaɓen shekarar 2027.

Ganduje ya sanar da haka ne a taron rantsar da sabbin shugabannin APC na Jihar Ribadu, ƙarƙashin jagorancin Cif Tony Okocha a ranar Asabar.

An zabi Okocha da sauran shugabannin su 23 ne a taron jam’iyyar na jiha da aka gudanar makonni biyu da suka gabata a birnin Fatakwal.

Ganduje, wanda ya samu rakiyar  sauran mambobin Kwamitin Zartarwa na Kasa guda 16, ya yi kira ga mambobin APC da su goya wa sabbin shugabannin jihar baya tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen Gwamna na 2027.

Ganduje ya yi nuni da nasarorin da APC ta samu a yankin Kudu maso Kudu, wanda a baya ake ganin yankin PDP ne, yana mai ishara da nasarar da APC ta samu a jihohin Kuros Riba da Edo.

Ya kuma nanata cewa Jihar Ribas ita ce hadafin APC a shekarar 2027.

“Mun karɓe jihohi biyu a yankin. Jihar Ribas ita ce muradinmu,” in ji Ganduje.

A jawabinsa, Shugaban APC na Jihar Ribadu, Cif Tony Okocha ya bayyana kwarin gwiwar jam’iyyar wajen karɓe mulkin jihar a 2027.

Ya yi kira ga haɗin kai ya kuma yi kira ga mambobin da su dawo jam’iyyar, yana mai cewa APC ita ce mafita.