Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle ya sha alwashin cewa za a zaƙulo tare da hukunta duk masu hannu a kisan Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Bawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktar ƴaɗa labaru ta ofishin ministan, Henshaw Ogubike.
- Tinubu ya rantsar da Kekere-Ekun sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya
- ‘Yadda muka shafe wata 2 a hannun ’yan bindiga muna cin garin rogo da gishiri’
Matawalle ya yi tir da kisan sarkin, tare da bayyana hakan a matsayin “aikin rashin imani kuma abin da ba za a amince da shi ba.”
Ya ƙara da cewa “za mu yi iyakar bakin ƙoƙarinmu domin ganin an hukunta waɗanda ke da laifi a lamarin.”
Sanarwar ta ce Matawalle ya umarci shugaban hafsoshin tsaron Nijeriya ya ƙaddamar da bincike kan kisan nan take tare da tabbatar da ganin an hukunta duk waɗanda ke da hannu cikin lamarin.
Ta ƙara da cewa “za mu yi bincike na ƙwaƙwaf wajen ganin an hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.”
A jiya Alhamis ne dai aka gudanar da sallar janaza ta ‘Salatul Ga’ib’, ga sarkin na Gobir, wanda ’yan bindiga suka hallaka, kasancewar ba a samu gawarsa ba.
Sai dai an samu nasarar karɓo ɗan marigayin, wanda ’yan bindiga suka ce su tare, wanda yanzu haka yake karɓar kulawa a asibiti.
A ranar Laraba ne labarin kisan sarkin ya fito bayan ya kwashe sama da mako uku a hannun ’yan bindiga.
Matsalar masu satar mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da addabar jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya, duk kuwa da ƙoƙarin da hukumomi suka ce suna yi wajen tabbatar da tsaro.
Sai dai kisan sarkin na Gobir na daga cikin munanan abubuwan da suka faru a kwana-kwanan nan da ke nuna cewa har yanzu ’yan bindigar na ci gaba da cin karensu babu babbaka.