Gamayyar kungiyoyin matasa kungiyar sun yi barazanar maka Gwamnatin Jihar Sakkwato a Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) kan yin sanadin kisan gillan da ’yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa bayan sun yi garkuwa da shi.
Gamayyar kungiyoyin matasan karkashin inwuar Ƙungiyar Matasan Afirka ta Neman Sasanci da Zaman Lafiya, ta zargi Gwamnatin Sakkwato da sakacin da ya haddasa kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gobir.
Shugaban ƙungiyoyin matasan guda 18, Dokta Suleman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana haka ne bayan wani taron kwana biyu da suka kammala.
Ya ɗora laifin kisan da ka yi wa Sarkin Gobir kan abin da ya kira halin ko-in-kula da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta nuna.
- ’Yan bindiga sun sace mutane 150 da shanu 1,000 bayan kisan Sarkin a Gobir
- Yadda aka yi jana’izar Sarkin Ningi
Don haka ya ba ta wa’adin mako biyu ta biya musu buƙatunsu ko kuma su maka ta a gaban kotun ICC.
Ya ce, buƙatun su ne: “A sallami kwamishinan tsaron jihar, a biya diyya ga iyalan Sarkin Gobir sannan gwamnatin jihar ta fito ta bayyana matsayinta kan kisan sarkin.
“Muna zargin Gwamnatin da yin sakaci ne saboda ita ce ta gayyaci Sarkin Gobir din zuwa Sakkwato domin halartar taro, amma ta gaza ba shi kariya.
“Uwa uba kuma, ta kasa kuɓutar da shi bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi.”
Kokarin wakilinmu na yin magana da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Sakkwato, Bello Sambo Danchadi da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Abubakar Bawa, bai yi nasara ba.
Dukkansu babu wanda ya ɗaga waya ko amsa rubutaccen sakon da aka tura masa.