Masarautar Gobir ta gudanar da Sallar Jana’iza ga Sarki Isa Muhammad Bawa ba tare da gawarsa ba, sakamakon kisan gilla da ’yan bindiga su yi masa.
Dan basaraken da aka sace su tare amma suka sako shi a daren Laraba ya ce ’yan bindigar sun binne gawar mahaifin nasa da suka kashe a ranar Talata.
Dubban jama’a ne suka halarci sallar sarkin da kwanansa ya kare bayan ya shafe kusan kwanaki 26 a hannun ’yan bindiga
Hotunan yadda aka yi Sallar Jana’izar Sarkin Gobir ba tare da gawarsa ba (Salatul Ga’ib) bayan samun labarin cewa ’yan bindiga sun binne gawarsa.
“Alhamdulillah game da rayuwar Sarki, muna alfahari da shi domin ya gudanr da rayuwarsa ne wajen hidimta wa al’ummarsa,” in ji shi.
Surajo ya bayyana godiya ga al’umma bisa yadda suka nuna musu kauna da tausayawa a wannan yanayi da kuma lokacin da aka sace sarkin.
Alhaji Isa ya rasu ya bar mata uku da yaya 18 da kuma jikoki.