✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC

Hukumar EFCC ta ce za a yi gwanjon motocin ne a Legas da Abuja da Fatakwal da Kano.

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC, ta sanar da shirin gudanar da gwanjon motoci kusan 900 da ta ƙwace a faɗin ƙasar.

EFCC ta ƙwato motocin ne waɗanda suka haɗa da na alfarma a binciken da take yi kan ayyukan da suka shaifi laifukan kuɗi da suka haɗa da cin hanci da halatta kudin haram da zambar intanet.

Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, ta ce za a yi gwanjon motocin ne guda 891 a ƙarƙashin wata dokarta ta 2004 da 2007 da kuma 2022.

Haka kuma, EFCC ta yi kira ga al’umma da su ci gajiyar gwanjon motocin, inda ta yi alƙawarin cewa za a gudanar da tsarin cikin adalci.

Hukumar ta ce za a yi gwanjon motocin ne a Legas da Abuja da Fatakwal da Kano, tare da haɗin gwiwar da waɗanda za su sa ido don ganin yadda abin zai kaya.

EFCC ta kuma wallafa adireshin intanet ɗin da za a iya duba motocin a sassa daban-daban.

Kazalika, ta saka ranakun da za a iya duben, waɗanda suka fara daga ranar Litinin 20 ga Janairu har zuwa Litinin ta sama 27 ga Janairun 2025, tare da lokutan da za a duba ɗin.