Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Filato Edward Ebuka, ya ce wasu jami’an runudunar za su yi amfani da bindiga don dakile tarzoma a zaben cike gurbi da za a yi a jihar.
Za a yi zaben kujerar Sanatan Filato ta Kudu ne a ranar Asabar 5 ga Disamba, 2020, domin cike gurbin Ignatius Longjan da ya rasu a 2019.
- Gwamnatin Filato za ta hukunta mutanen da suka fasa rumbunan ajiye abinci
- Hukuma ta sasanta mazauna iyakar Kaduna da Filato
- Ba za mu bari Filato ta sake fadawa cikin rikici ba —Lalong
- Yadda aka kashe jami’in tsaron DSS a jihar Filato
Kwamishinan ya samu wakilcin Yinusa Ishak, a taron masu ruwa da tsaki da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shirya.
Ishak ya ce rundunar ba za ta rika zura ido bata-gari na cin karensu ba babbaka a lokacin zabe ba.
Ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar ya ce babu wanda za a bari ya kada kuri’a ba tare da ya sanya takunkumi ba.
Sannan ya ce dole ne mutum ya bude fuskarsa kafin kada kuri’a saboda gudun kada wani ya jefa kuri’a a madadin wani.
Ya kuma jaddada cewa dole ne a bi matakan kariyar cutar COVID-19 don kauce wa yaduwarta.
Jami’in ya ce duk wanda aka samu da alamar cutar za a dauke shi zuwa inda za a ba shi agajin gaggawa.