Shugaban Amurka Joe Biden ya amince da tura daruruwan dakaru zuwa Somaliya domin tunkarar mayakan al-Shabab da suka addabi kasar.
Wannan na nufin Shugaba Biden ya janye matakin da tsohon Shugaba Donald Trump ya dauka a lokacin da yake kan mulki inda ya janye kusan sojoji 700 wadanda ke a kasar.
- Matashiya ta yi karar Mahaifinta saboda kin aura mata wanda take so
- NAJERIYA A YAU: Wuraren Da Rashin Tsaro Zai Hana Noma A 2022
Jami’an leken asiri na Amurka sun yi kiyasin cewa al-Shabab na da kusan mambobi 10,000 duk da cewa mambobin na cikin Somaliya, amma Amurkar na ganin cewa za su iya kai mata hari.
Shekara biyu da suka gabata, al-shabab ta kai mummunan hari kan sansanin sojin saman Amurka da ke Kenya.
Babu tabbaci kan ko sojoji nawa Shugaba Biden zai tura, sai dai rahotanni sun ce suna daga cikin sojojin kundunbala na musamman da za a kai cikin Somaliya.