Sakataren Kwamitin Shura na kungiyar Limamai da Alarammomi na Jihar Kurosriba, Kyaftin Rilwan Liman ya ce kwamitinsa zai yi matukar bakin kokarinsa ya ga ya fidda kitse cikin wuta, waje samar da tabbataccen zaman lafiya da fahimtar juna musamman tsakanin Musulmin Jihar Kurosriba da wadanda ba Musulmi ba.
Kwamitin, an dora masa alhakin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba kuma ya yi duk abin da zai yi na ganin an taimaka wa mata ’yan asalin Jihar Kurosriba da aka mutu aka bar su da marayu kana kuma da ma wadanda suka Musulunta danginsu suka kore su.
Da yake zantawa da Aminiya jim kadan da kafa kwamitin, sakataren kwamitin, Kyaftin Rilwan Liman wanda shi ne babban limamin masallacin barikin soja na Eburutu da ke Kalaba, ya ci gaba da cewa: “Za mu yi dukkan iya bakin kokarinmu, mu ga mun kamanta adalci, mun tabbatar an samu dorewar zaman lafiya tsakanin mabanbanta addinan nan biyu sannan kuma hada kai na al’ummar Musulmin Jihar Kurosriba, su zama masu magana da murya daya,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Za mu yi dukkan kokari mu ga mun hada kai da sauran kungiyoyin sa-kai na addini, kamar su Jama’atu da kwamitin koli na harkokin addinin Musulunci. Har wayau za mu ci gaba da kokarin ganin duk Musulmi mazauna kudanci mun rika yin magana da murya daya, domin nuna bambanci ko wariya tsakaninmu ba shi da amfani.”
Kwamitin shura shi ne irinsa na farko da aka kafa tun bayan zuwan al’ummar Musulmi jihar, shekaru masu yawa.