Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa za su sayar da dukan kadarorin da aka kwace amma har yanzu babu wanda ya zo ya ce mallamakarsa ne.
Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake jawabi a masarautar Daura a lokacin da suka kawo masa ziyara a gidansa da ke Daura.
Kadarorin dai sun hada da kayayyaki da filaye da gidaje da sauran su. Sannan ya kara da cewa akwai kadarorin da Gwamnatin Tarayya ta kwato daga da dama a cikin kasar nan.