✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu sasanta rikicin Rasha da Ukraine — Shugabannin Afirka

Shugabannin sun hada da na Congo Brazzaville da Masar da Senegal da Uganda da Zambia.

Shugabannin kasashen Afrika sun amince su yi balaguro zuwa Rasha da Ukraine a cikin wannan wata na Yuni da zummar sasanta rikici tsakanin kasashen biyu da suka shafe sama da shekara guda suna yaki da juna.

A watan da ya gabata ne, shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, shugabannin Rasha da Ukraine wato Vladimir Putin da Volodymyr Zelensky sun amince su karbi bakwancin taron tattaunawar zaman lafiyar da zai samu halartar shugabannin kasashen Afirka shida.

Wata sanarwa da ofishin Ramaphosa ya fitar ta ce, shugabannin na Afirka sun yi wata ganawa ta yanar gizo a ranar Litinin da ta gabata tare da fayyace matsayarsu ta gabatar da tayin dakatar da musayar wuta ga Rasha da Ukraine da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu.

A yayin wani taron manema labarai, shugaba Ramaphosa ya ce, dole ne shugabannin na Rasha da Ukraine su yi musu cikakken bayani game da mahangarsu ta yakar juna da kuma sharuddan da suke so su zayyana kafin samun jituwa a tsakaninsu.

Ramaphosa ya kara da cewa, za su gabatar da tasu mahangar a matsayinsu na shugabannin Afrika a yayin zaman sasanta Rasha da Ukraine din, inda kuma ya jaddada muhimmancin sauraren korafin kasashen biyu.

Shugabannin kasashen na Afirka da za su halarci wannan zama sun hada da na Congo Brazzaville da Masar da Senegal da Uganda da Zambia.

Kodayake Firaministan Masar ne zai wakilci shugaban kasar, sannan akwai yiwuwar shugaba Yoweri Museveni na Uganda shi ma ya gaza halartar taron saboda cutar Covid-19 da ta kama shi.