✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kwace filin duk bankin da ke kin ba da sabbin kudade —Zulum

An gagara samun tsabar kudi na N100,000 a karamar hukumar Gubio , in ji Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ba da umarnin kwace takardun filayen duk bankin da ke kin ba wa mutanen jiharsa sabbin tardun Naira da aka canza.

Zulum ya ba da umarnin ne bayan an gagara samun takardun sabbin kudi na Naira 100,000 a fadin Karamar Hukumar Gubio ta jihar.

Ya ce, “Duk bankin da ya yi ki loda sabbin kudin a ATM domin mutanenmu su samu, za mu kwace takardun filinsa.”

“Jiya na je garin Gubio mai mutum 70,000, amma an kasa samun N100,000 na takardun sabbin kudi ko tsoffi a fadin karamar hukumar.

“Ragon da a baya ake sayarwa N100,000 ya koma N35,000 saboda yadda mutane ke neman tsabar kudi ido rufe, sannan wasu maara imani na shiga kauyuka suna cutar muane,” in ji gwamnan.

A ranar Juma’a gwamnan ya bayar da umarnin bayan ya yi zagaye a rasssan wasu bankuna domin ganin irin wahalar da jama’ar jiharsa ke sha wajen bin layin sabbin kudi saboda rashin sabbin kudin.

Gwamnan ya bayyana bacin ransa ne bayan ya iske dogon layin mutane a reshen wani banki wanda ATM guda daya tal daga cikin ATM da ke reshen ne ke ba da kudi.

“Na je ATM sun fi 1o, amma daya kadai ke da kudi,” in ji shi.

Ya ce, “alakawa ne kadai ke bin dogon lai, ban ga masu kumbar susa ba, an ce wasu ma un karfe 3 na asuba suka fio don su kama lai, ko abinci ba su ci ba.

“Rashin sabbin kudin da ma ofaffin na shafar harkokin kasuwanci a jihar, kuma jama’a na shan wahala,” in ji Zulum.

Ya ce mun biya albashin kusan Naira biliyan biyar, amma mutane sun kasa samun kudadensu, saboda wasu injinan AM ba sa aiki.

“Ba mu da matsala da tsarin CBN ko kayyade cirar N20,000, tun da an ce kowa zai iya cirar N20,000 to me zai hana kowa samu?” in ji shi.

Don haka gwamnan ya rokin Babban Bankin Najeriya ya yi abin da ya dace wajen abbaar da wadauwar sabbin ukarudin kudaden ga ’yan kasa.