✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za Mu Kawo Karshen Dokar Kullen IPOB —Soludo

Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce gwamnatinsa za ta soke dokar kullen ranakun Litinin da haramataciayr kungiyar (IPOB) ta kakaba a jihar. 

Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce gwamnatinsa za ta soke dokar kullen ranakun Litinin da haramataciayr kungiyar (IPOB) ta kakaba a jihar. 

Soludo ya ya bayyana wa bikin ranar ma’aikatan gwamnati ta 2022 da aka gudanara ranar Talata cewa gwamnatinsa ta yi nasarar kawar da bata-garin da suka mamaye kananan hukumomi takwas na jihar watanni kadan bayan zamansa gwamana a watan Maris.

Ya ce, “A baya an ce wai ’yan bindiga ne da ba a san ko su waye ba, amma magana ta gaskiya an san ko su wane ne, don daga cikinnmu suke.

“Dole mu koma aiki da zuwa makaranata sau biyar a sati ba sau hudu ba, domin muna asarar kashi 20 na cigaban da ya kamata a ce mun samu.”

A watan Maris ne gwamnan ya sanar da kawo karshen dokar ta IPOB, sai dai tsoro ya hana mutane watsi da ita.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa zai yi karin kashi 10 na albashin ma’aikata daga shekarar 2023, baya ga maye gurbin kyautar shinkafar Kirsimeti da gwamnatin baya ke yi da rabon N15,000 ga ma’aikata da ’yan fansho.