✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Za mu kawar da ayyukan ta’addanci a Katsina —Shugaban ’Yan Sanda 

Hakan ba za ta sake faruwa ba, an yi na farko kuma an yi na karshe.

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu Abdullahi, ya tabbatar wa jama’a cewar za su yi iyaka kokarin su wajen ganin cewa an kawar da ayyukan ta’addanci musamman a Jihar Katsina.

Babban Sufeton ya furta hakan ne a ranar Laraba a hedkwatar ’yan sandan Jihar Katsina a wata ziyarar gana wa da jami’an da ya kai domin tattauna matsaloli gami da samar da hanyoyin da za’a shawo kan wadannan ayyuka na ta addanci da suka addabi Jihar da makwabciyarta Jihar Zamfara.

Babban Sufeton bayan jajanta wa al’ummar Jihar ta Katsina dangane da sace Daliban Makarantar Sakandiren Kimiya da ke garin Kankara, ya ce “an yi na farko kuma an yi na karshe.”

Ya ce, “Hakan ba za ta sake faruwa ba da dukkan sauran ayyukan ta’addancin da suka addabi wasu yankuna na kasar.”

Babban Sufeton ‘Yan sandan yayin da yake jawabi a hedkwatar ‘yan sanda a Jihar Katsina.

Kafin shigar su tattaunawar sirri da sauran jami’ansa, Babban Sufeton ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai tare da ba su duk wata gudunmuwa domin kawo karshen matsalolin tsaron duba da cewa, harkar tsaro wani lamari ne wanda ya rataya a kan kowa.