✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu karbi duk wata kujera a Sakkwato ba tare da wahala ba – Abdallah Wali

Sanata Abdallah Wali dan takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a Jam’iyyar PDP da abokan takararsa suke korafi kan lashe zaben fidda gwanin da ya lashe, lamarin…

Sanata Abdallah Wali dan takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a Jam’iyyar PDP da abokan takararsa suke korafi kan lashe zaben fidda gwanin da ya lashe, lamarin da ya sa Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo ya je don sasantawa, ya kira taron manema labarai kwana daya da ziyarar don shaida musu abin da ya gudana:

Aminiya: A zaman da aka yi da Mataimakin Shugaban kasa don sasantawa wace matsaya aka cimma?
Wali: Matamakin Shugaban kasa Alhaji Muhammad Namadi Sambo ya zo nan Sakkwato ne domin ya tattauna da shugabannin jam’iyya da wadanda suka yi takarar kujerar Gwamna da majalisar jiha, ya tattauna da mu, ya gaya mana wadanda suka ci zabe mu dauka Allah ne Ya ba su wadanda ba su ci ba su dauki haka Allah Ya so, kuma mu yi aiki tare domin
jam’iyya ta samu nasara, ya ce mu da muka ci zabe dole mu tafi da wadanda suka fadi da mutanensu ba wani bambanci in aka samu nasarar kafa gwamnati tamu suna da hakki a kanta.
Duk da bambancin ra’ayi kan maganar sasantawa a samu nasara don zama ne na ba da magana da hakuri ga wadanda ba su samu nasara ba, saboda an riga an kai wa hukumar zabe sunayen ’yan takara na jam’iyyu babu lokacin sauya ’yan takara. Kuma ni na tabbatar wa Mataimakin Shugaban kasa cewa za mu tafi tare da wadanda ba su samu nasara ba don ciyar da jiharmu gaba.
Aminiya: Kana ganin jam’iyyarku na iya lashe zaben Gwamna a zaben mai zuwa?
Wali: Mun shirya mu shiga zaben 2015 tsaf kamar koyaushe da ikon Allah za mu iya nasara kamar sauran shekaru da suka gabata don har yanzu muna nan da karfinmu musamman samun Bafarawa a tare da mu, za mu karbi duk wata kujera a Jihar Sakkwato ba da wata wahala ba domin an gaji da wannan gwamnati kowa ka gani a jihar canji yake so.
Aminiya: Wace irin kasawa kake ganin wannnan gwamnati ta yi da har kake son ka canja ta?
Wali: Tarbiyyar matasa ta lalace, akwai bukatar gyara, in za mu gaya wa junanmu gaskiya, tabbas akwai bukatar kawo gyara ga al’amuran rayuwar jama’a, dole mu shiga cikin wannan yakin don taimakon kanmu da kanmu da yaranmu, kan abubuwan da suka shafi kasa. Ka duba ka gani hukumar kidididga ta kasa ta bayyana jiharmu da mafi talauci a kasar nan, to me muka rasa, jihar da ke da fiye da kashi 90 na kasar noma, na tabbata zan iya canja jihar a harkar noma. Don za mu taimaki manoma da duk abin da suke nema, za mu fadada Madatsar Goronyo ta wadaci dukkan jiharmu da ruwa har a iya noman rani a kowace karamar hukuma. A sha’anin ilimi hukumar kula da ilimi ta kasa ta fitar da bayani cewa jihar da ta kafu kan ilimi yanzu ita ce mafi koma baya a harkar ilimi, don haka za mu fito da hanya mafi dacewa tun daga makarantun firamare har zuwa jami’a.
Aminiya: Mataimakin Gwamna Muntari Shagari ya ce shi ne ya fi dacewa da takara don an ba shi tikitin tsayawa takara babu hamayya, me za ka ce?
Wali: Da farko dai jam’iyyarmu ta amince mu sayi fom din takara mu hudu a Abuja, muka zo Kaduna aka tantance mu, ka ga maganar an yi wa wani alkawari ba ta taso ba, a shekarar 2007 a lokacin ina minista a matsayin jagoran jam’iyya da ni aka yi zaman karbar kujerar takarar Gwamna daga Muntari aka bai Magatakarda a wannan zaman ba inda aka yi maganar ga wanda zai gaji Wamakko, wannan maganar kawai ana yin ta ne da Tony Anine aka yi wancan zama kuma kwanakin baya ya zo nan Sakkwato don sasanta ’yan takara kuma Muntari ya tuna masa karbar tikitinsa da aka yi a wancan lokacin amma bai gaya masa sun yi masa alkawari ba. In har an yi alkawarin ya fito da takardar yarjejeniya da aka yi ba wai ya rika magana da ’yan jarida cewa an yi masa alkawarin tikitin Jam’iyar PDP ba hamayya ba. Gwamna Yero (na Kaduna) ma wasu sun yi takara da shi balle Mataimakin Gwamna, ya kamata mu yi wa kanmu adalci, a zo a yi wanan tafiya don samun nasarar jam’iyya.