Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya fada wa takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, cewa yana fatan yaukaka dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa (KCNA) ya rawaito cewa a ranar Litinin Shugaba Putin ya aike wa Kim din wasika kan bikin cika shekara 77 da kawo karshen mamayar Japan a yankin Koriya, inda ya ce kawancen zai amfani kasashen biyu.
- ’Yan bindiga sun yi kisa, sun sace mutane da dama a kasuwar Kogi
- Jamus za ta sanya wa masu amfani da iskar gas sabon haraji
Putin ya ce, “Rasha da Koriya ta Arewa za su ci gaba da fadada dangantaka a tsakaninsu, wacce za ta kara inganta tsaro a yankin Koriya da ma yankin Arewa maso Gabashin nahiyar Asiya.”
Shi ma Kim ya aike wa Putin wata wasikar inda ya ce Yakin Duniya na Biyu ya dada karfafa dangantakar Rasha da Koriya ta Arewa bayan cin galaba a kan Japan, wacce ta mamaye yankin Koriya daga 1910 zuwa 1945.
Kodayake KCNA bai fayyace su wa kasashen ke nufi da abokan gabar ba a cikin wasikun nasu, amma a baya sun sha yin amfani da kalmar a kan Amurka da ’yan kanzaginta.
Kim dai ya yi hasashen cewa alakar kasashen biyu za ta inganta la’akari da yarjejeniyar da suka cim ma lokacin da ya gana da Putin a 2019.
A watan Yulin da ya gabata dai kasar Koriya ta Arewa ta goyi bayan ballewar wasu yankunan kasar Ukraine a matsayin masu cin gashin kansu kamar yadda Rasha ta yi.
Lamarin dai ya sa a lokacin Ukraine ta yanke alakarta da Koriyar don nuna rashin jin dadinta a kan matakin.