Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Ta’annutin Kudi ta EFCC, Ibrahim Magu ya ce tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro biyu wandanda suka ki yarda a kama su za su shiga hannu nan da ’yan kwanaki kadan.
Tsohon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta SSS, Ita Ekpeyong da kuma tsohon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta NIA, Ayo Oke sun ki yarda su kai kansu hukumar EFCC don su amsa tambayoyi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.