Hukumar Kula da Bin Dokokin Muhalli ta Kasa (NESREA) ta ce tana da hurumin gurfanarwa tare da hukunta masallatai da majami’un da suke takura wa jama’a ta hanyar amfani da amsakuwa yayin ibada.
Babban Daraktan Hukumar, Farfesa Aliyu Jauro ya bayyana cewa yawan surutu daya ne daga cikin manyan kalubalen da muhalli ke fuskanta.
- Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya lalace a daji
- ‘Na yi wa matar aure fyade a kullum na tsawon watanni biyar’
A zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Lahadi, shugaban Hukumar ya ce yawan surutun na barazana ga tsirrai, dabbobi da ma bil’Adama.
“Yawan wannan surutun kan haifar da matsalolin lafiya da dama da suka hada da Hawan Jini da ma sauran cututtuka da dama. Saboda haka a matsayinmu na hukuma, muna da rawar da za mu taka wajen takaita yawan surutun.
“Abin da muke yi shine tabbatar da ana bin doka. Mutane na aiwatar da abubuwa da dama da ke takura wa muhalli, mu kan karbi korafe-korafe da yawa.
“Alal misali, wurare irinsu majami’u da masallatai har ma da masana’antu na damun mutane da surutu matuka, wanda kuma idan muka sami korafi mu kan je mu same su mu tattauna a kan matsalar.
“Mu kan basu shawarar hanyoyin da zasu yi aiki ba tare da takura wa jama’a ba, mu kan yi amfani da doka kuma a inda bukatar hakan ta taso,” inji shi.
Farfesa Aliyu ya kuma yi kira da a kara dagewa wajen wayar da kan jama’a a kan illar domin su gane barazanar da haken ke haifarwa ga muhalli.
Daga nan sai ya ce hukumar na da hurumin gurfanar da kowanne mutum ko kungiyar da ta ki bin dokokin. (NAN)