✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Filato ta hana sanya shingaye a masallatai da coci-coci

Mutfwang ya umarci coci-coci da masallatai su rika neman izinin gina su daga Hukumar Raya Birnin Jos da Kewaye (JMDB)

Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, ya haramta sanya shingaye a coci-coci da masallatan da suke toshe hanyoyin mota a jihar.

Gwamnan ya ce, wannan umarni yana nufin rage cinkoson ababen hawa da tabbatar da tsaron lafiyar jama’a a jihar.

Baya ga wannan hani, gwamnan ya umarci dukkan coci-coci da masallatai su rika neman izinin gina su daga Hukumar Raya Birnin Jos da Kewaye (JMDB).

Wannan sanarwar ta fito ne a wata wasika mai dauke da kwanan wata 13 ga Yuni, 2024, wadda Janar Manajan Hukumar JMDB, Mista Hart Bankat ya sa wa hannu.

Wasikar bangare ne na aiwatar da Dokar Gwamna Mai lamba 003 da Gwamna Mutfwang ya sanya wa hannu.

Tuni aka aike da ita ga shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI).

Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, reshen Jihar Filato, Dokta Salim Musa Umar, ya tabbatar da karbar wasikar.

Abubuwan da ke cikin wasikar sun nemi cibiyoyin addini, su ba da hadin kai, don sarrafa zirga-zirgar ababen hawa da tabbatar da shirye-shiryen ajiye motoci da kyau a wuraren ibada.

“Bisa Dokar Gwamna Mai lamba 003 da Gwamna Caleb Mutfwang ya sa wa hannu a ranar 1 ga Maris, 2024, don kula da zirga-zirgar ababen hawa da gine-gine, ana ba da umarnin hana toshe hanyoyin ababen hawa.

“Ya kamata dukkan wuraren ibada, su samar da wuraren ajiye motoci da suka dace, a lokutan da ake gabatar ibada ga jama’arsu,” in ji wasikar.