Masarautar Saudiyya za ta yi wa masallatai masu dadadden tarihi a yankin Makkah garambawul domin kara inganta su.
Yarima Mai Jiran Gado Mohamed Bin Salman ne ke jagorantar aikin da zummar gyara masallatan da kuma kara wa gininsu karfi, kasancewa an gina su tun daruruwan shekaru da suka gabata.
- Atiku ya ziyarci Kano saboda komawar Shekarau PDP
- Yadda yajin aikin ASUU ya girgiza tattalin arzikin al’ummar Zariya
Masallatai 30 ne a fadin Saudiyya ne za a yi wa garambawul a rukuni na biyu na shirin farfado da al’adu da masallatai masu dadadden tarihi da nufin dawo da martabar kasar a matsayin cibiyar Musulunci da kuma al’adunta da tarihinta.
Ga jerin masallatan da za a gyara a yankin Makkah:
1- Masallacin Al-Baiah da ke kusa da wurin jifa a Mina shi ne za a fara yi wa garambawul a rukuni na biyu na aikin, wanda Yarima Mai Jiran Gado, Mohamed Bin Salman yake jagoranta.
An gina shi tun zamanin ne Halifancin Abu Ja’afar Al-Mansour, kuma za a bar girmansa yadda yake, inda yake daukar mutum 68, fadin harabarsa kuma sukwaya mita 457.
2- Masallacin Al-Fath, wanda aka ruwaito Manzon Allah (SAW) ya yi Sallah a cikinsa ranar da ya ci Makkah da yaki, kimanin shekara 1440 da suka gabata.
Yanzu masallacin yana yankin Al-Jamoum, kuma za a kara masa girma ya rika daukar mutum 333, fadinsa kuma sukwaya mita 553.50.
3- Masallacin Abu Inbeh wanda aka gina shekara 900 da suka wuce a yankin Harat Al-Sham da ke Jiddah, mai girman Sukwaya mita 339.98.
Idan aka kammala aikin, girmansa zai ragu zuwa sukwaya mita 335.31 kuma zai rika daukar mutum 357.
4- Masallacin Al-Khadr mai tazarar kilomita 66 daga Masallacin Harami. An gina shi shekara 700 da suka gabata. Idan aka kammala gyaran zai dauki mutum 355, fadinsa kuma sukwaya mita 355.
5- Masallacin Al-Jubail wanda aka gina shekara 300 da suka gabata. Za a bar girmansa yadda yake cin mutum 45, harabarsa kuma sukwaya mita 310.
Daga: ArabNews