Kungiyar Kiristoci ta Najeria (CAN), ta nesanta kanta da wasu malaman Coci-Coci da suka halarci bikin kaddamar da tsohon gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima da aka yi a matsayin dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar APC a zaben badi.
Kungiyar ta ce wadanda suka halarci kaddamarwar ba ’ya’yanta bane, wasu mutane ne na daban da basu alaka da coci suka yi shiga irin ta fada-fada suka je taron domin a ce kiristoci na goyon bayan wannan takara.
- Mene ne bambancin ’yan siyasa da ’yan ta’adda?
- An kama matashin da ya yi wa kanwarsa fyade sau 2 a Gombe
Rahotanni sun ce mutanen su kimanin 20 cikin shiga na limaman dariku daban-daban ne suka halarci taron a matsayin masu nuna goyon bayan Shettima da kuma dan takarar Shugaban Kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda kungiyar CAN take kalubalanta.
Kungiyar Kiristocin na kalubalantar lamarin na tsayar da musulmi biyu a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar APC mai mulki, wanda ta ke ganin ya saba wa tsarin siyasar kasar da kuma tsarin bai wa manyan addinan kasar biyu damar wakilci.
CAN ta kuma ce ba za ta goyi bayan hakan ba har a tsakanin mabiyanta wanda ka iya shafar nasara jam’iyyar a zabe mai zuwa.
Sai dai a hirarsu da ‘yan jaridu yayin taron, limaman sun ce sun zo ne a matsayin wakilai daga gamayyar kungiyoyin limaman coci-coci na kasa.
Joseph Hayab na kungiyar CAN na cewa, “Da alamar tambaya a irin shigarsu, daga gani hayo su aka yi”.
A nasa martanin, Bayo Onannuga, kakakin yakin neman zaben Tinubu yana mai cewa, “wadannan limaman ba na bogi bane, ba dai fitattu ne da kowa ya san su bane. Shi ya sa a ke ganin na karya ne.”