✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu tilasta wa kowa ya koma APC ba — Tinubu

Babu wanda zai iya tilasta wa kowa ya tsaya a inda bai so, APC a shirye take ta karɓi ƙarin ’yan Najeriya da ke son…

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki masu cewa gwamnatinsa na ingiza ’yan Najeriya wajen bin tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa ba za a iya zargin mutane kan zaɓar jam’iyya ba.

Da yake jawabi a wajen taron ƙoli na jam’iyyar APC  karo na farko da aka yi a ranar Alhamis, da ya gudana a fadar shugaban ƙasa a Abuja, shugaban ya ce “jam’iyya ɗaya ce ke mulki”.

“Ga waɗanda har yanzu suke tunanin fita daga jam’iyyarsu, ƙasar nan taku ce, ku riƙe ta, ga masu maganar tsarin jam’iyya ɗaya, jam’iyya ɗaya ce ke mulkin Najeriya, ba za ku zargi mutanen da ke shirin ficewa a jam’iyyar ba.

“Na yi farin ciki da abin da muke da shi kuma ina tsammanin ƙari. Haka lamarin yake. Muna cikin tsarin mulkin demokraɗiyya.”

Ya ce, babu wanda zai iya tilasta wa kowa ya tsaya a inda bai so, ya ƙara da cewa APC a shirye take ta karɓi ƙarin ’yan Najeriya da ke son shiga jam’iyya mai mulki.

Ya ce, “Suna ganin jam’iyyar siyasa ta gaza, amma da jajircewarku, ba mu yi ƙasa a gwiwa ba, mu ne masu ci gaba, za mu yi sojan gona, ku ci gaba da yin aiki tuƙuru… Ina saurarenku ba su ba.

“Muna da damar da za mu sa Afirka ta kasance mai mai ci gaba, amma ina roƙonku da a ci gaba da tafiya tare. Ga waɗanda ba zan iya ba ma muƙaman siyasa ba, ku yi haƙuri, za ku yi farin cikin shiga wannan jam’iyya.”