Kamfanin mai na Najeriya (NNPC) ya bankado yadda masallatai da coci-coci da jami’an gwamnati ke da hannu a satar mai.
Shugaban NNPC, Mele Kyari, ya bayyana damuwar bisa girmar matsalar fasa bututan mai da ake yi da hadin bakin kungiyoyin addini da sauran mutane a yankunan da layin bututun ya wuce.
- Yajin aikin ASUU: Rashin kwarewar Ministan Ilimi ne —Atiku
- DAGA LARABA: ‘Yan Ta’adda Na Fada A Ji A Najeriya.
Mele Kyari ya bayyana cewa a wani wuri da tsawonsa bai wuci mita 200 ba, NNPP ta gano wurare 295 da barayin mai suka ja bututum mai.
Shugaban kamfanin a yi zargin cewa a wasu wuraren an janyo bututun mai ta barauniyar hanya zuwa masallatai da coci-coci.
Ya ce NNPC ya samu nasarar ce da taimakon da ya samu daga jami’an tsaro na ciki, bisa umarnin Babban Hafsan Tsaron Najeriya.
Ya bayyana takaici bisa yadda barayin man suke jawo wa Najeriya asarar makudan kudaden shiga da ya kamata ta samu daga kasuwannin duniya.
A cewarsa, kamfanin ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma yana samun nasarori wajen magance matsalar satar danyen man ta watsu har a tsakanin shugabannin addini da kungiyoyin addini da sarakuna da jami’an gwamnati da sauran al’umma.
A cewarsa, kawo yanzu an kama kwalekwale masu gudu 30, kwalekwalen katako 170 da manyan motoci 37 daga hannun masu fasa bututun mai, kuma gwamnati ta dauki matakin kona su gaba daya.
An kuma cafke mutum 122, ciki har da wasu fitattun mutane a tsakanin watan Afrilu da Agusta, kuma an mika wasunsu ga Hukumar EFCC, mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa.