Mutane 20 sun rasu, wasu 3,000 sun rasa muhallansu sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a garin Gashin da ke jihar.
Ibtila’in ya rutsa da su ne a cikin mako biyu da suka gabata a garin da ke Karamar Hukumar Bade ta jihar.
Shugaban Karamar Hukumar, Babagana Ibrahim, ya ce gwamnati na kokari samar da kayan agaji da magunguna ga mutanen da ke gudun hijira.
Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawo musu dauki, musamman na abinci da sauransu domin daƙile barkewar annoba a sansanin da suke gudun hijira.
Ya ce, “kwanan nan ana yawan ruwa, gidaje na rushewa. A safiyar yau kadai mutane hudu sun mutu a Gashuwa.
“Yanzu haka manyan hanyoyin Gwamnatin Tarayya sun yanke, wanda hakan ya zama matsala ga ma’aikata jinƙai wajen kai ɗauki.”
Shugaban karamar hukumar ya umarci masu gine-ginen kasa da su tashi domin guje wa rushewarsu.