✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu hukunta masu hannu a harin Tudun Biri —Hafsan Tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christoper Musa ya ce rundunar za ta hukunta duk sojan da aka samu da laifi a harin Tudun Biri

Babban Hafsaon Tsaron Najeriya, Janar Christoper Musa ya ce rundunartsaro za ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a harin da jirgin soji a kauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Janar Musa ya sanar a ranar Juma’a cewa da zarar rundunar ta kammala bincike kan harin, duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

ya shaida wa manema labarai a Hedikwatar tsaro da ke Abuja cewa babu yadda za a zura ido wani ya yi irin wannan aika-aika ba tare da an hukuna shi ba.

A cewarsa, “a aikin soja ba ma kare masu laifi, saboda haka za mu yi komai a fili, babu rufa-rufa.

“Mun sha hukun dakarunmu da ke rundunar Operation Hadin Kai, wasunsu koun soji ta yanke musu hukuncin dauri a kurkuku.