Gwamnatin Tarayya ta ce ta fara aiki da jihohi domin samar da gidaje masu rangwamen kudi da ’yan Najeriya masu karamin karfi.
Babban sakatare a ma’aikatar ayyuka da samar da gidaje ta kasa, Mahmud Mamman, shi ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar farko na taron kungiyar masu ruwa da tsaki a harkokin samar da gidaje da bunkasa birane na kasa, da ke gudana a Kaduna.
Babban sakataren ya kara da cewa ” shirin samar da gidaje na ma’aikatarmu zai taimaka wa wadanda ba su da galihu a kasar nan su samu matsuguni”.
Ya kuma yi karin bayani kan sabon shirin gwamnatin Shugaba Tinubu na fara gina gidaje masu rangwamen kudi a kowacce jiha da hadin gwiwa da gwamnatin jihohi.
- NLC na neman goga wa Tibubu bakin jini —Fadar Shugaban Kasa
- HOTUNA: Ayyuka sun tsaya cak a Majalisa da NNPC bayan fara yajin aikin NLC
A cewarsa, “mun rubuta wasika ga jihohin kasar nan muna bukatar da su ba mu fili da za mu gina irin wadannan gidaje ga ’yan Naijeriya”.
Kan maganar sanin adadin gidajen da ake bukata, Mamman ya ce tuni hukumar kidaya ta kasa ta fara tattara musu alkaluma.