Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ba wa ’yan Najeriya tabbacin samun sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan Majalisun Tarayya da ke gudana a yau a kan kari.
Idan za a iya tunawa a shekarar 2019 sai da aka kwana biyu da kammala zaben shugaban kasa kafin INEC ta sanar da sakamakonsa.
- Zaɓen 2023: Wane ne Atiku Abubar na PDP?
- Zaɓen 2023: Wane ne Bola Ahmed Tinubu na APC?
- Zaɓen 2023: Wane ne Peter Obi na LP?
- Zaɓen 2023: Wane ne Rabiu Kwankwaso na NNPP?
ِAmma shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ba da tabbacin cewa a wannan karon hukumar za a fitar da sakamakon da wuri.
Game da fargabar cewa tsarin sauyin kudi na Babban Bankin Najeirya (CBN) zai kawo wa cikas wajen gudanar da zaben 2023, shugaban hukumar ya ce kawo yanzu ba su da wata matsala ta wannan bangaren.