Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano, (PCACC), ta ce za ta fasa shagunan ’yan kasuwar da ke taskance kayan abinci na nufin cuzgunawa al’umma ta kuma rabar da kayan kyauta.
Shugaban Hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri na musamman da aka yi da shi a safiyar Litinin a gidan rediyon Freedom da ke Kano.
- Damfara ta miliyan N450 aka yi rana guda —Ummi Zee-Zee
- Kwamishinan da aka yi garkuwa da shi a Anambra ya kubuta
- NAFDAC ta karrama Shugaban Hukumar KAROTA a Kano
- An bude cibiyar bayar da fasfo cikin gaggawa a Abuja
“Duk wanda muka kama yana boye kaya, za mu fasa shagon mu raba wa jama’a,” a cewarsa.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake alakanta tsadar kayan masarufi da annobar COVID-19, amma ya ce hakan ba zai hana hukumar hukunta duk ’yan kasuwan da ke neman jefa al’umma cikin halin ni-yasu ba.
Rimin Gado ya ce binciken PCACC ya gano cewa annobar COVID-19, ce sanadin hauhawar farashin wasu kayayyakin.
A cewarsa, kamfanoni da dama, musamman masana’antun sukari a Jihar Kano sun ce za a samu sukari da zai wadaci al’umma har zuwa karshen watan azumin Ramadan mai kamawa.
Tun gabannin gabatowar watan azumi na Ramadan, wasu kayayyakin masarufi suka fara yin tashin gwauron zabo a jihar ta Kano da ma wasu jihohin Najeriya.